Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hikayata 2021: Labarai uku da suka cancanci lashe gasar
Alƙalan gasar Hikayata ta 2021 sun gama zaman tattaunawa don fitar da labarai uku da za su karɓi kyautar ta farko da ta biyu da ta uku.
Alƙalan sun yi zaman nasu ne a Abuja inda suka duba labarai 25 da aka rairaye daga labarai sama da 400 da mata da dama daga sassan duniya suka aiko don shiga gasar ta mata zalla.
A halin yanzu dai sun zaɓi labaran 'Butulci' da labarin 'Haƙƙina' da kuma labarin 'Ramat'.
Sai dai ba su bayyana wanne daga cikin waɗannan labaran ne zai fitar da gwarzuwar gasar ta bana ba, sai a wani bikin karramawa da BBC za ta shirya a Abuja, babban birnin Najeriya za a bayyana wacece gwarzuwar.
Jagorar alƙalan ta bana, Dokta Hauwa Muhammad Bugaje, malama a sashen nazarin harsuna a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta bayyana cewa "Gaba ɗaya labaran nan sun yi tarayya a saƙo guda na halin da ake ciki yanzu, na matsalolin rayuwa, halin tagayyara da fyaɗe da tsaro. Waɗannan labarai sun zama zakaran gwajin dafi a gasar Hikayata ta bana."
Labarin Ramat
Labari ne kan wata mata mai suna Ramat da ta shiga aikin ƴan sanda a ƙasar Hausa kuma ta haɗu da mijinta a bakin aiki wanda shi ma ɗan sanda ne.
Sun yi aure sun shimfiɗa rayuwa mai kyau mai cike da albarka kuma sun samu rabon ɗa ɗaya tal.
Sun nuna wa ɗan nasu gata har girmansa inda suka kai shi Turai karatu sai dai dawowarsa ke da wuya ya aikata wani mummunan laifi wanda ya jefa iyayensa cikin matsanancin hali.
Ramat ta shiga halin gaba kura baya sayaki - wato ta kuɓutar da ɗanta ko ta riƙe martabar aikinta na babbar jami'ar ƴan sanda.
Daga ƙarshe ta ɗauki matakin da ya mai karatu ba zai taɓa tsammani ba sai dai labarin ya yi kyakkayawan ƙarshe don kuwa an samu mafita.
Labarin Haƙƙina
Wannan labari ne mai sosa rai a kan wata budurwa da ta fuskanci babban ƙalubale na rayuwa.
Inda take tunanin za ta ɗan ji sanyi sai ta fuskanci ƙuna, ta shiga halin ha'ula'i.
Labarin Haƙƙina ya taɓo jigo na fyaɗe da tsoron tsangwama da wahalhalun gidan aure da rashin girmama ƴa mace.
Dokta Hauwa Bugaje ta ce marubuciyar wannan labarin ta yi amfani da wani salo na rubutu inda ta bai wa tauraruwar labarin hanyar sama wa kanta mafita duk da matsanancin halin da take ciki.
Labarin Butulci
Labarin Butulci labari ne kan wata mata da ƙaddara ta faɗa mata aka yi garkuwa da ita, ga shi tana da ƙaramin ciki.
Tana hannun masu garkuwa tana cike da fargaba da zaƙuwar ta sanar da mijinta samun cikin nata.
Bayan ta kuɓuto daga hannun masu garkuwa da mutane ta isa gida a wahalce - sai dai ba ta samu bayyana wa maigidan nata kyakkayawan fatan da take rawar ƙafar sanar da shi ba saboda wani mummunan labari da ta gamu da shi.
Butulci labari ne mai ɗaukar hankali da ban tausayi.
An shigar da labarai sama da 400 a gasar ta bana inda aka miƙa su ga alƙalai na musamman wanda suka tankaɗe suka rairaye su aka mayar da su guda 25.
Wajen tantancewar dai an yi amfani da ƙa'idojin shiga gasar, musamman game da adadin kalmomi, da bin ƙa'idar rubutu, da amfani da daidatacciyar Hausa, da kauce wa amfani da kalaman da ba su dace ba da zarge-zarge, da ma tabbatar da cewa labarin ƙagagge ne.
Waɗannan 25 ɗin ne alƙalan suka duba kuma suka fitar da uku da suka yi zarra da 12 da suka cancanci yabo.
Dukkan labaran 15 dai za a karanta su nan gaba a rediyo a kuma saka su a shafukanmu na intanet da na sada zumunta.
Gwarzuwar za ta samu kyautar kudi dalar Amurka 2,000 da lambar yabo; wadda ta zo ta biyu kuma za ta karɓi kyautar kuɗi dala 1,000 da lambar yabo; sannan wadda ta hau matsayi na uku za ta karɓi kyautar kuɗi dala 500 da lambar yabo.