Abin da 'yan Najeriya ke cewa kan kasafin kudin 2022 na Buhari

Lokacin karatu: Minti 4

Ƴan Najeriya na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu kan kasafin kudin shakarar 2022 da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar wa Majalisar Dokokin ƙasar a ranar Alhamis.

A ranar Alhamis ne Shugaba Buhariya gabatar da kasafin na 2022, wanda ya haura naira tiriliyan 16, da ya ce zai mayar da hankali wajen kammala ayyukan da gwamnatinsa ta fara.

Majalisun tarayyar Najeriyar za su fara nazari kan ƙudurin kasafin kuɗin 2022 ɗin a ranar Juma'a.

Sai dai, kasafin kuɗin zai zo da ciyo ƙarin bashi har kimanin naira tiriliyan shida, don cike giɓin da za a samu.

Tuni ƴan ƙasar da suka haɗa da ƴan majalisa da ƴan siyasa da ƙwararru da ma sauran mutane suka fara bayyana ra'ayoyinsu.

Honarabul Abubakar Yunus, dan majalisar wakilai ne na tarayya, ya shaida wa BBC cewa akwai kyakkyawan fata dangane da kasafin kuɗin na 2022 da Buhari ya gabatar musu, kuma suna fata a gyara kura-kuran da aka gani a kasafin kudin 2021.

"Muna son wannan ya kasance ya inganta tsarin yadda ake tafiyar da ayyukan gwamnati musamman ma abin da zai kawo wa ƙasa dogaro da kai, da kuma inganta ƙalubale na wajen samun kuɗaɗen shiga.

Ɗan majalisar ya ce akwai abubuwa da dama da suka birge shi game da ƙudurin kasafin da Shugaba Buhari ya gabatar.

"Abin da ya burge mu shi ne akwai waɗansu abubuwa da aka yi la'akari da su waɗanda gaskiya idan aka yi za su ta da wasu kura-kurai wadanda aka yi a baya. Kuma akwai kyakkaywan fatan inganta abin da ake aiwatarwa a 2021.

Yayin gabatar da kasafin 2022 dai Shugaba Buhari ya yi bita kan yadda ake kashe kasafin kuɗin shekarar da ake ciki ta 2021, kamar misali na yi wa ƙasa aikace-aikace da suka haɗa da inganta tsaro da inganta zamantakewa da samar da na'urori da abuwan ci gaba.

Honarabul Yunus ya ce a wannan fannin gwamnati ta yi rawa gani, "saboda a halin da muke cikin nan tun ma kafin ya zo, mun ga yadda suka saki kuɗaɗe inda aka kashe kai 60 cikin 100 na ainihin abin da aka ƙuduri niyyar yi a 2021.

"Idan dai aka daure aka tafi a haka to gaskiya kwalliya za ta biya kuɗin sabulu," kamar yadda ya ce.

Shugaba Buhari dai ya ce kashi ɗaya cikin uku na kasafin kudin 2022 ɗin da bashi za a yi shi, amma ɗan majalisa Yunus ya ce hakan ba shi da wani aibu, saboda gwamnatin na bin komai sau da ƙafa kamar yadda aka tsara.

"Sau tari idan aka yi maganar bashi sai ka ga cikin mutane ya ɗuri ruwa amma ƙarƙashin mulkin Shugaba Buhari ta yi rawar gani, don duk bashin da take ci da kuma bain da ta ayyana wa kanta za ta dinga biya shekara-shekara, to ta yi rawar gani a nan.

"Zuwa yanzu tana bin komai sau da ƙafa, ma'ana duk shekara idan ta ce za ta ciyo bashi kaza kuma za mu biya, to tana hakan," in ji dan majalisar.

Ya ce abin da ba a so shi ne a ciyo bashi a zo a yi ta kashe kuɗin ba tsari, don haka majalisar ta yi na'am da tsarin.

Me sauran ƴan Najeriya ke cewa?

Ra'ayoyi sun bambanta a kan wannan batu a tsakanin ƴan kƙasar, yayin da wasu ke yaba wa gwamnati, wasu kuma kushe ta suke yi musamman kan batun ciyo bashi don cike giɓin kasafin kuɗin.

Ƙungiyoyin fararen hula kamar SERAP mai sa ido kan ayyukan ƴan majalisa a ƙasar ta ce: "Muna so Shugaba Buhari ya yi gaggawar ajiye rahoton shirin karɓo bashi don cike giɓin kasafin kuɗin ƙasar.

"Za mu fafata don matsa wa gwamnatin dakatar da wannan ciwo bashin marar kan gado, da kawo ƙarshen cin hanci da kuma rage yawan kuɗaɗen da ake kashewa a gwamnati."

A shafin tuwita wani Hamma @HAHayatu ya ce: "Gwamnati Buhari da ba ta san ciwon kanta ba za ta sake ciyo bashin naira tiriliyan shida a 2022 wanda jikoki sa tattaɓa kunninsa ne za su biya.

"Abin takaicin ma shi ne mafi yawan kasafin kudin da aka gabatar za a kashe ne a kan al'amuran yau da kullum, wannan gwamnatin ta ƙi ta rage yawan kuɗaɗen da take kashewa."

Daga shafin BBC Hausa Facebook

Bayan wani neman jin ra'ayi da muka yi a shafin BBC Hausa Facebook ranar Alhamis da yamma, mutane da dama sun yi ta tsokaci.

Bashir Sahal Yakubu Nguru ya ce: "Muna fatan kasafin kudin shekara ta 2022 da Shugaba Buhari ya gabatar wa majalisa ya kawowa "yan Najeriya saukin rayuwar da suke ciki."

Ahmad Bajoga: "Tsawon shekaru bakwai da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi yana gabatar da kasafin kudi ga Majalisan Dokokin kasar, babu wani abu na zahiri da talakan Najeriya ya amfana da shi."

Dayyabu Akilu B B ya ce: "Gina 'yan kasa kafin gina kasa, ta yadda abinci zai wadata, kazalika ta yadda talauci da fatara za su ragu sosai, sannan a yi amfani da su wajen inganta harkar ilimi ta yadda talaka zai samu damar karatu cikin sauki, yin hakan zai matukar tasiri wajen kawo ci gaban kasa da kuma samar da zaman lafiya mai dorewa."