Boko Haram ta mamaye garuruwa da dama a jihar Neja

Rahotanni a jihar Neja da ke arewacin Najeriya na cewa ƙungiyar Boko Haram ta mamaye garuruwa da dama na jihar, inda suke bai wa mazauna ƙauyuka kuɗi tare da sanya su cikin mayakansu.

Wasu mazauna yankin sun ce mayaƙan sun mamaye wasu ƙauyukan da ke cikin ƙaramar hukumar Shiroro suna yi wa mutane wa'azi, al'amarin da ya jefa jama'ar yankin cikin fargaba da tashin hankali.

"Ƴan Boko Haram suna tara mutane suna yi musu wa'azi, suna kuma raba kuɗi a garin Kurebe da Kwaki," kamar yadda wani mazauni yankin ya shaida wa BBC.

Wannan na zuwa, watanni shida bayan Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello ya yi gargaɗin cewa ƙungiyar Boko Haram ta kafa tuta a wasu ƙananan hukumomin jihar guda biyu.

Gwamnan jihar Abubakar Sani Bello wanda ya tabbatar da kasancewar Boko Haram a jihar a watan Afrilu, ya ce mayaƙan sun kafa tuta ne a ƙananan hukumomin Kaure da Shiroro.

Wasu rahotanni kuma yanzu sun ambato shugaban ƙaramar hukumar Shiroro da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Neja Alhaji Sani Idris suna tabbatar da ɓullar mayakan na Boko Haram a wasu yankunan na Neja.

Shugaban ƙaramar hukumar Shiroro Suleiman Chukuba, ya shaida wa Kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa ƴan Boko Haram sun mamaye aƙalla ƙauyuka takwas daga cikin 25 na yankin.

"Akwai ƴan Boko Haram da dama da yankin ƙaramar hukumar Shiroro," in ji Chukuba.

Wasu rahotanni sun ce kusan ƙauyuka 500 ne mayaƙan suka mamaye a ƙaramar hukumar Shiroro.

Wasu mazauna yankin da BBC ta zanta da su sun ce ƴan Boko Haram sun ɓulla a makwabtan garuruwa ciki har da Mashekari da Lukafe da Kusaka da Sabon Gida da kuma Kwaki Chukuba. Kuma Mayaƙan har sun fara yi wa mutane hukunci.

Boko Haram sukan shigo gari su tara mutane a waje suna wa'azi da zartar wa mutane hukunci," a cewar wani mazauni yankin.

Ya ƙara da cewa mayaƙan sun samu wurin zama ne bayan janye jami'an tsaro a yankin nasu.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Neja Alhaji Sani Idris ya fadawa Reuters cewa gwamnatin jihar da kuma jami'an tsaro sun dukufa don dakile bazuwar 'yan Boko Haram din zuwa wasu yankuna.

Tun a watan Agustan 2020 aka fara bayar da rahoton ɓullar Boko Haram a Neja da ke makwabtaka da Abuja babban birnin Najeriya bayan wani bidiyo da ke iƙirarin nuna mayaƙan suna gabatar da saƙon gaisuwar Sallah.

Kusan fiye da shekara 12 jami'an tsaron Najeriya ke yaƙi da Boko Haram. Har yanzu ƙungiyar na ci gaba da zama barazana a Najeriya da ƙasashen da ke kewaye da Tafkin Chadi duk da mutuwar shugaban ƙungiyar Abubakar Shekau.

A baya-bayan na kusan ƴan Boko Haram 8,000 ne suka miƙa wuya ga hukumomin Najeriya, sai dai bullar mayaƙan masu tayar da ƙayar-baya a jihar Neja da ke kusa da babban birnin Najeriya Abuja, wani al'amari ne da ke sake fito da buƙatar yin hubbasa don kakkeɓe duk wata barazana daga mayaƙan da da har yanzu suke addabar yankin arewa maso gabashin Najeriya fiye da tsawon shekara 10.