Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Eunice Osayande: Abin da ya sa za a sa wa wani titi a Turai sunan wata 'karuwa' 'yar Najeriya
- Marubuci, Daga Megha Mohan
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Gender and identity correspondent
Birnin Brussels ya ce zai sanya wa wani sabon titi sunan wata 'yar Najeriya ne da ta yi karuwanci a baya, domin dai nuna mahimmanci da mata suke da shi a Belgium.
Hukumomin birnin sun ce za a sanya wa titin sunan Eunice Osayande, wadda wani abokin huldarta 'mara imani' ya caka mata wuka a watan Yuni 2018.
Bayan romon baka da aka yi mata na samun aiki da kuma rayuwa mai kyau a nahiyar Turai, abin da ya janyo Ms Osayande babban birnin Belgium a 2016.
Mutanen da suka yi wa Ms Osayande romon baka suka kawo ta Turai sun ce za su mayar da ita tauraruwar fina-finai, amma a zahiri, kawai safarar ta suka yi.
Ba jimawa da isarta Brussels ta fada harkar karuwanci. An nuna mata cewa masu kai mutane Turai na bin ta bashin da ya kai dalar Amurka 52,000 na kai ta Turai da aka yi da kuma kama mata haya da aka yi.
'Yan makonni gabanin mutuwarta, ta tattauna da kungiyar ba da agaji ga karuwai inda ta fada musu cewa tana fuskantar cin zarafi da barazana yayin gudanar da ayyukanta.
Tana kuma tsoron kai kara wajen 'yan sanda saboda ba ta hanyar da ta dace ta je kasar ba, don ka da a kama ta.
A watan Yunin 2018, aka kashe Ms Osayande mai shekara 23, lokacin da wani abokin huldarta ya caka mata wuka sau 17 a yankin Gare du Nord.
Nan da nan karuwai suka jagoranci wata zanga-zanga a Brussels. Suna bukatar a samar musu da yanayi mai kyau da za su ci gaba da gudanar da ayyukansu cikin tsari irin na shari'a.
Ba a haramta karuwanci ba a Belgium, amma kuma babu wata dokar kasa a kansa.
Wata darakta a kungiyar kare masu karuwanci ta UTSOPI Maxime Maes, su ne suka shirya macin.
"Mutuwar Eunice ta tayar da hankali matuƙa, musamman a wurin 'yan ciranin da ke zaune a kasar ba bisa ƙa'ida ba a yankin da take huldarta," ta shaida wa BBC
"An rika samun karuwar cin rafin mata musamman wadanda ke karuwanci a yankin."
Wani matashi dan shekara 17 aka zarga da kashe Ms Osanyande kuma har yanzu yana jiran shari'a. An kama mutum hudu daga cikin masu safarar mutanen, kuma a watan Janairun wannan shekarar aka yanke musu hukuncin zaman gidan yari na shekara hudu.
Da sanya sunanta a kan wannan sabon titi, hukumomin birnin sun ce za su janyo hankalin duka "matan da aka manta da cin zarafinsu da aka yi ta hanyar safararsu talala da wadanda ake nuna musu tsana a fili.
Titin zai zama na farko da aka taba sanya wa sunan karuwa a fadin kasar, kamar yadda wata kafar watsa labarai ta kasar ta bayyana.
Titin da ke arewacin birnin Brussels na daga cikin sabbin tsare-tsaren da kasar ta bullo da su ta sanya wa wurare da yawa sunan mata.
Tuni hukumomin suka sanya wa wasu tituna da yawa sunayen wasu fitattun mata, ciki har da mai fadan nan Yvonne Nèvejean da Andrée De Jongh sai wata gada da aka sanya wa sunan Suzan Daniel, wata mai fafutuka a Begium.
Titin wanda ake gina wa, za a buɗe shi nan da watanni masu zuwa.
Mahukuntan sun ce za a gayyaci karuwai da 'yan ci rani su gabatar da makalu ranar buɗe titin.