Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An kubutar da daliban makarantar Kayar Maradun a Zamfara
Rahotanni daga jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya sun tabbatar da cewa an kubutar daliban makarantar sakandaren Kayar Maradun da aka sace kwanaki.
A wani bidiyo da BBC ta samu daga jami'an jihar ta Zamfara, an ga Gwamna Bello Matawalle yana magana da wasu dalibai mata daga cikin wadanda aka kubutar din, yana tambayar su yanayin da suka samu kansu a hannun 'yan bindigar.
Duk da rashin sadarwa da intanet da ake fama da aka katse sua jihar a wani mataki na yakar 'yan bindigar, wani jami'in gwamnatin Zamfaran da ya aiko wa BBC bidiyon ya ce tun jiya Lahadi da marece aka kubutar da yaran.
Ya kara da cewa sai da jami'an suka je jihar Sokoto mai makwabtaka sannan suka iya aikawa da bidiyon.
Hukumomin sun ce an tarbi daliban ne a ranar Lahadi da yamma a fadar gwamnatin jihar, amma ba su bayyana yadda aka yi aka kubutar da su ba, walau ta hanyar biyan kudin fansa ne ko ta hanyar sasanci.
A ranar 1 ga watan Satumban nan ne 'yan bindiga suka kai hari makarantar ta maza da mata da ke karamar hukumar Maradun kuma suka sace dalibai da dama.
Mazauna garin Kayar Maradun sun shaida wa BBC Hausa cewa 'yan bindigar sun kai harin ne da safiyar Laraba a lokacin da wasu daliban suke rubuta jarrabawar 'Mock' ta 'yan aji biyar.
Daga baya ne hukumomin jihar suka ce dalibai 70 aka sace yayin da wasu malaman makarantar kuma suka ce 76 ne.
Me bidiyon ya nuna?
A cikin bidiyon, an ga Gwamna Matawalle tsaye a gaban wata motar bas da dalibai mata ke ciki, inda suka gaishe shi, shi kuma yake tambayarsu ko sun san shi, sai suka ce a'a.
"To ba ku san Matawalle ba?" Sai kuma suka saka dariya suka ce "ah, mun san ka." Daga nan sai suka sake yi masa sabuwar gaisuwa cikin nishadi da fara'a.
"Mun gode sosai, Allah Ya saka da alheri, Allah Ya biya ka," a cewar yaran suka fada cikin hada baki a tare. Gwamna kuma ya dinga amsaw
Shi ma Gwamna Matawalle cikin irin tasa fara'ar ya dinga amsawa da "amin, amin." Sai yake tambayarsu "an dawo min da ku lafiya babu wacce aka taba ko?"
Nan da nan 'yan matan suka ce "a'a babu wacce aka taba, ba a yi mana komai ba, sai dai sun dinga yi mana barazana."
"Sai su dinga nuna mana wuka, har da rami suka tona suna nunawa suna cewa sai sun yanka mu," in ji yaran.
Gwamna ya sake jaddada tambayarsa da cewa "babu dai wacce aka taba ko? Suka sake amsa da "eh." Sai ya ce "to Alhamdulillahi, na gode," su ma suka ce sun gode sosai.
Daga nan ne sai gwamna da tawagarsa suka nufi mota ta gaba mai dauke da dalibai maza.