Yadda Afrika Ta Yamma take matsa ƙaimi a yaƙi da ta'addanci a yankin Sahel

    • Marubuci, Daga Paul Melly
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Mai sharhi kan Afrika

A daidai lokacin da Chadi za ta janye dakarunta da rage yawan dakarun Faransa daga yankin Sahel mai girman gaske a yankin Yammacin Afrika - inda kungiyoyin masu iƙirarin jihadi ke ci gaba da ƙaddamar da hare-hare kan fararen hula da sojoji ba tare da nuna bambanci ba - sabon shirin yaƙi da ta'addancin na dab da fara aiki.

Ministocin tsaro na ƙasashen G5 Sahel - Burkina Faso da Chadi da Mali da Mauritania da Nijar - na shirin karfafa ayyukan haɗin gwuiwa na sojoji da tattaunawa.

Za a mayar da hankali a al'ummomin da ke noma da kiwo a yankin nan mai iyakoki uku, inda Burkina Faso da Nijar da Mali suka gamu kuma hare-haren masu tayar da ƙayar baya suka fi ƙarfi.

A taron tsaron na wannan makon da aka gudanar a Niamey, babban birnin Nijar, inda aka kammala tattauna sabbin hanyoyin ƙasashen G5 Sahel na jan ragamar yadda za a fara ayyukan.

Faransa za ta ja baya inda za ta zama mai tallafawa kawai, bayan da Shugaba Emmanuel Macron a kwanan nan ya sanar da cewa ayyukan kasarsa na yaƙi da ta'addanci na Operation Barkhane zai zo ƙarshe inda za a rage yawan sojojin Faransar a yankin Sahel daga 5,100 zuwa 2,500-3,000 a watanni masu zuwa.

Haka kuma, Nijar da Mali da Burkina Faso sun yi fama da matakin Chadi na janyewa ba zato ba tsammani a watan Agusta don rage dakarunta a iyakokin uku daga sojoji 1,200 zuwa 600.

Gwamnatin Chadi ta riƙo wadda ke mulkin ƙasar tun bayan mutuwar Shugaba Idriss Déby a watan Afrilu, ta yanke shawarar dawo da rabin sojojin gida don tsaron cikin gida.

Sun ƙunshi:

  • Boko-Haram a Najeriya da wani ɓangarenta na Iswap, wanda ke ci gaba da kai hare-hare a al'ummu da ke tafkin Chadi
  • Bazuwar tasirin rikicin da ake yi tsakanin ƴan tawaye da gwamnati a makwabciya Jamhuriyar Tsakiyar Afrika
  • Sannan a hamadar arewa da Chadi, ƴan bindiga da ke iya yin barazana - duk da ƙoƙarin gwamnati na amincewa da tsarin tsaro da Libya.

Sai dai suk da ra'ayin gwamnatin riƙon Chadi ya dace, me zai zama makomar yaƙi da masu iƙirarin jihadi a yankin tsakiyar Sahel?

Kashe-kashe a kan babur

Ƙungiyar Human Rights Watch ta yi ƙiyasin cewa fararen hula 420 aka kashe a wannan shekarar a yammacin Nijar kawai.

Hare-hare na baya-bayan nan ma haka.

Ranar 16 ga watan Agusta wasu ƴan bindiga a kan babura sun abka ƙauyen Dareye-Daye, wanda dama an kai masa hari a watan Maris kuma aka kashe mutane 37.

Bayan kwana biyu fararen hula 47 da wasu jami'an tsaro sun mutu lokacin da aka kai hari kan wani jerin gwanon motocin soji tsakanin Dori da Arbinda a arewacin Burkin Faso.

Amma a zahiri sojojin Chadi da aka janye kwanan nan na da horon aiki da manyan kayan aikin soji - amma duk da haka ba su dace da rikicin mai kewaya ba a yankin tskaiyar Sahel, inda watannin damina na watan Yuni zuwa Satumba ke hana shiga wasu yankunan.

Shugaba Déby ya tura dakarun da aka janye zuwa yankin tsakiyar Sahel a watan Fabrairu.

Faransa ta sha matsa masa ya sa wasu dakarunsa cikin rundunar haɗin guiwa ta G5 Sahel - shirin da a ƙarƙashinsa ne dakarun ƙasashen ƙungiyar ke haɗa kai su yi aiki tare a yaƙi da ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi.

A bara aka shirya aika dakarun na Chadi - amma aka samu tsaiko lokacin da Déby ya mayar da hankali kan yaƙi da Boko Haram a cikin gida.

Ana kammala wannan aiki, ya ɗaura ɗamarar taimakawa - matakin da ya ƙarfafa matsayinsa a yankin kuma ya ɗaga martabarsa a Faransa, inda hakan ya sa Faransar ta kauda kanta daga mulkin kama-karya da yake yi a Chadi.

Sai dai ko da motocin yakin Chadi suka isa yankin mai iyakoki uku, salon faɗan ya sauya.

Sojojin rundunar Mali misali, sun koma hawan babura don bin maharan a guje.

Don haka ficewar sojojin Chadin bai shafi sabon ƙoƙarin na G% ba - kuma sojojin Chadin 600 da za su kasance a yankin za su ci gaba da taimakawa.

Rundunar Tarayyar Turai za ta taka muhimmiyar rawa

Sabawa da rage yawan dakarun faransa na da muhimmanci.

Mista Macron ya daɗe yana fuskantar ƙalubale bisa muradansa na dogon zango a yankin Sahel.

A lokacin da ya sanar da cewa Operation Barkhane zai zo a ƙarshe a jajiberin taron ƙoli na G7, ya jaddada cewa sojojin Faransa za su ci gaba da zama a yankin.

Cikakkun bayanai sun biyo baya ranar 9 ga watan Yuli, a wani taron manema labarai na haɗin guiwa da sabon shugaban Nijar Shugaba Mohamed Bazoum.

Rundunar Turai ta Takuba, wadda aka kafa a shekarar da ta gabata kuma take aiki da rundunar Mali, za ta taka muhimmiyar rawa.

Wani ɓangare na rundunar Faransa da aka rage za su haɗu da Rundunar takuba - wadda ke da runduna ta musamman daga Faransa da Estonia da Czech da Sweden da Italiya, da jiragensu na helikwafta.

Romania ta yi alƙawarin ba da dakarunta kuma ana sa rai wasu ƙasashen za su taimaka su ma.

Takuba, wadda take Niamey, za ta mayar da hankali ne kan yankin mai iyakoki uku tare da rundunonin G%.

Faransa za ta bar wata ƴar karamar runduna wadda za ta kula da ayyukan yaƙi da ta'addanci kuma za ta zama babbar mai taimakawa ayyukan rundunar Tarayyar Turai da ke horar da rundunonin yankin Sahel.

Haka kuma, sansanonin Faransa a Ivory Coast da Senegal za su ci gaba da kasancewa saboda fargabar yunƙurin masu iƙirarin jihadi na son kutsawa ƙasashen gaɓar tekun Afrika ta Yamma.

Amma da gwamnatocin G% da Faransa duk sun amince samar da ci gaba ga al'ummomi a yankin sahel, ya zama wani ɓangare mai muhimmanci.

Masu ba da agaji a Turai da dama yanzu na ware kuɗin agaji a kasafin kuɗinsu.

Sai dai barzanar ita ce amfani da kuɗin wurin yin ayyukan da za su amfani mutanen yankin.

Kuma rundunonin sojin Burkina Faso da Nijar da mali tare da kawayensu na Yamma na buƙatar sake gina tsaro da zai ba da damar tattalin arziƙi da ci gaba su haɓaka.

Paul Melley jami'i ne a ɓangaren Shirin Afrika na Chatham House da ke Landan.