Abin da wasu ƴan Najeriya ke cewa kan cire Nanono da Mamman

A wani abu da ba a saba gani ba, kwatsam sai aka ji Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sallami ministoci har biyu.

Wannan lamari ya kasance abin mamaki matuka musamman ga ƴan Najeriyar da ke zaton akasarin ministocin da Shugaban ya nada a 2015, da su zai karasa mulkinsa.

Sai ga shi an fara da wadanda aka nada a 2019, wato Saleh Mamman ministan wutar lantarki da kuma Sabo Nanono da ba su wuce shekara biyu da yan kwanaki kan kujerar ba.

Kuma da alama Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ba zai tsaya kan wadannan ministocin biyu ba, domin kuwa ana ganin cewa zai kara waiwayar wasu daga cikin ministocin nasa domin ya sallame su.

Mai magana da yawun shugaban Najeriyar Malam Garba Shehu ne ya tabbatar wa da BBC hakan a wata hira inda ya ce wannan saukewar somin taɓi ne, "akwai wadanda za su biyo baya."

Sai dai tun bayan da aka sanar da sauke ministocin biyu, jama'a da dama musamman a shafukan sada zumunta suka soma bayyana ra'ayoyinsu kan wannan lamari.

Me ƴan Najeriya ke cewa game da sauke ministocin?

Mabiya shafukan BBC a Facebook da Twitter da sauran shafukanmu sun ta bayyana ra'ayoyi daban daban dangane da wannan lamari inda wani mai bibiyarmu Abdullahi Aminu ya ce shi ba maganar sauke ministoci ke damunsa ba, maganar tsaro ce abin damuwa inda ya yi fatan samun zaman lafiya a Najeriya.

Shi kuwa Alhaji Saminau Daura jajanta wa ministocin da aka sauke ya yi tare da yi wa waɗanda suka maye gurbinsu fatan alkhairi

Sai kuma Ibrahim Muhammad Ɗansule wanda shi kuma cewa ya yi Allah sa wannan matakin da Shugaba Buhari ya ɗauka ya kawo ƙarshen matsalar tsadar kayan abinci da kuma matsalar wutar lantarki

'Da Naira Talatin mutum zai ci ya ƙoshi a Kano'

Da alama wani abu da ƴan Najeriya da dama ba su manta da shi ba shi ne wani kalami da tsohon ministan aikin gona Sabo Nanono ya taɓa yi inda ya ce mutum zai iya cin abinci ya ƙoshi da naira talatin a Kano.

Hakan ya sa har aka buɗe wani gidan cin abinci a Kano wanda ake sayar da kwanon abinci naira 30, sai dai bayan wasu watanni kuma an rufe gidan abincin.

Toh a shafinmu na Facebook ma, mun samu dubban saƙonnin mutanen da suka ce ba za su taɓa mantawa da waɗannan kalaman na tsohon ministan ba.