Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shugaba Biden da Taliban kowa na cewa ya yi nasara a Afghanistan
Shugaba Joe Biden na Amurka ya kara kafewa kai da fata wajen kare matakin da ya dauka na kawo karshen shekara 20 da Amurka ke yaki a Afghanistan, da cewa bukata ta biya, ta kawar da Al Qaeda tun shekara goma baya.
Yayin da Taliban da ficewar sojojin Amurkar ta ba wa damar sake kama iko da kasar ke cewa ta yi galaba a kan Amurkar.
Duk da cewa ba wata manufa ba ce ta sauya a kan abin da Shugaba Biden din ya fada tun a baya game da ficewar sojojin Amurkar daga Afghanistan ba, matakin da ya bude kofa ga 'yan Taliban suka yi kome na sake damke mulkin kasar,
wanda Amurkar ta jagoranci kwace wa daga wurinsu shekara ashirin baya, abin da ya zamo tamkar hannun karba hannun bayarwa.
Sai dai a wannan karon shugaban ya jajirce kai da fata cewa matakin abu ne da ya kamata, domin Amurka a cewarsa ta riga ta samu biyan bukatarta tun da ta ga bayan kungiyar Al Qaeda tun shekara goma da ta wuce.
A yayin wani jawabi da ya yi da aka watsa kai tsaye ta talabijin, a kan yakin mafi dadewa da Amurka ta yi, wanda a jiya a hukumance aka kawo karshensa da ficewar sojojin Amurkar, a wa'adin karshen watan Agusta, Mista Biden ya ce a rikicin da aka shafe shekara ashirin ana yi ko da kafin yanzu aka yi wannan ficewa to da zai zama da matsala.
Shugaban ya kira kwashe mutanen da aka yi daga kasar a matsayin gagarumar nasara ta daban, duk da cewa akwai dubban 'yan Afghanistan da ke hankoron ficewa amma an bar su:
Ya ce: ''Mun yi nasara a kan abin da muka tsara yi a Afghanistan, tun shekara goma da ta wuce. Sannan muka tsaya na tsawon wata shekara goma. Lokaci ya yi da za a kare yakin nan. Wannan sabuwar duniya ce.
Barazanar ta'addanci ta watsu a duniya, ta wuce Afghanistan.
Ya ce: ''Babban abin da yake wajibi a kan shugaba, a ra'ayinsa shi ne kare Amurka, ba wai daga barazanar 2001 ba, a'a kare ta daga barazanar 2021 da ta gobe.''
Mista Biden ya kuma sake sukar magabacinsa Donald Trump, saboda kulla yarjejeniya da Taliban, wadda ya ce ta tilasta masa a kan lokacin ficewar.
Tare da kara jaddada cewa tuni hakarsu ta cimma ruwa game da yakin.
Kuma ya ce kare yakin ya bijiro da bukatar yin gagarumin sauyi a manufofin waje na Amurka
Ya ce dole ne su rika tsara manufofin da za su iya cimmawa karara, ba wadanda za su dauki tsawon lokaci har ma su wuce abin da ya kama ce su ba.
Ya ce wannan mataki a kan Afghanistan, ba kawai a kan Afghanistan ba ne. Abu ne a kan kawo karshen zamani na manyan ayyukan soji, domin fuskantar wasu kasashen.
Ya ce barazanar da suke fuskanta ta zamanin yanzu ta hada da China da Rasha da barazana ta intanet, haɗi da 'yan ta'adda da ke sauran wurare - a Afirka da Gabas ta Tsakiya.
Duk da wannan kafewa da shugaban na Amurka yake ta yi, matsalarsa a kan Afghanistan din ba ta kau ba.
Domin akwai jan aikin da ke gabansa na tsugunar da dubban 'yan gudun hijirar Afghanistan din.
Da yadda zai kare gwamnatinsa daga 'yan majalisar dokoki kan yadda yakin ya zo karshe, abin da 'yan hamayya, 'yan Republican suka kuduri aniyar ganin ya yaba wa aya zaki a kansa a siyasarsa.
To amma wannan mataki ne da shugaban ya jima yana son dauka kamar yadda wasu ke gani. Kuma yana ganin shi kam abu ne da ya kwanta masa a rai, da ba zai yi nadamar dauka ba, wanda kuma yake fatan Amurkawa da yawa a karshe za su tuna da shi.
Sai dai kuma yayin da duk ake wannan ita kuwa Taliban tana murna ne da ficewar Amurkar daga Afghanistan.
Tana bayyana hakan a matsayin nasara da za ta zama darasi ga sauran masu mamaya.
Amma kuma yayin da suke gyara zamansu a kan mulki daga kungiyar tawaye zuwa mai gwamnati, shugabanninta na nuna cewa suna son kulla alaka mai kyau da Amurka da sauran duniya.
Kuma wannan shi ne irin ra'ayin Ministan Harkokin Waje na Qatar, Sheik Mohammed bin AbdulRahman bin Jassim Al -Thani, wanda a yayin wani taron manema labarai da takwaransa na Jamus a Doha, ya ce lokaci ya yi da kasashe za su yi alaka da Taliban ko kuma a koma 'yar gidan jiya.
Yana mai cewa ware su ba shi ne abin yi ba. Kuma tafiya da su tare ba shi ne abin bayar da fifiko ba a kai.