Zimbabwe: An kama wanda ake zargi da hannu a mutuwar wata yarinya yayin haihuwa a coci

    • Marubuci, Daga Shingai Nyoka
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar BBC, Harare

Ƴan sanda a Zimbabwe sun kama wani mutum mai shekaru 26 bayan da wata yarinya ta mutu yayin haihuwa a coci, lamarin da ya harzuka ƴan kasar da masu fafutikar kare hakkin dan adam.

Rahotanni sun ce Memory Machaya, mai shekara 15, ta mutu kuma an binne ta a watan jiya a wani wurin bauta da ke birnin Marange na gabashin kasar.

Ƴan sanda kuma na tsare da iyayenta.

Lamarin ya bayyana karara yadda ake cin zarafin kananan yara, yayin da rahotanni suke cewa an tilasta wa yarinyar barin makaranta domin ta yi aure.

Ana zargin Iyayen yarinyar da yin ƙarya game da shekarunta tare da bayar da ƴarsu ƴar shekara tara ga mutumin, Hatirarami Momberume.

Yana fuskantar tuhumar yi wa yarinya fyaɗe.

Uku daga ciki da ake zargi ba su yi magana ba kawo yanzu.

Mutuwar Anna a ranar 15 ga watan Yuli bayan bikin ranar haihuwarta, ta jawo hankali jama'a game da yadda ake yi wa kananan yara auren wuri a cikin Cocin Apostolic da ke Zimbabwe, wadda akasari ba ta amincewa da magungunan asibiti.

Wannan yanayi ne ya yi sanadin mutuwar Anna da kuma ƴan sanda da hukumar kula harakokin jinsi na binciken yadda aka binne ta.

Tuni dai wasu mutane suka kaddamar da kamfe a shafukan intanet da ke kira a yi adalci game da kisanyarinyar wanda a turance suka yi wa lakabi "justice for Memory Machaya" kuma kawo yanzu fiye da mutum 92,000 sun sanya hannu kan takardar kamfe din.

Fitacciyar 'yar kasar Zimbabwe da ke kare hakkin mata Everjoice Win ta ce lokaci ya yi da za a matsa lamba kan "masu mulki su tabbatar da bin doka ko kuma su yi sababbin dokoki" kan batun.

Ta wallafa wani sako a shafinta na Tuwita da ke cewa ba a kallon manyan mata da kananan mata "a matsayin cikakkun mutane, wadanda suke da 'yanci... na yin abin da suka ga dama da jikinsu."

Dokokin Zimbabwea sun amince a aurar da yarinyar da ta kai shekaru 18, yayin da macen da ta kai shekaru 16 ana kallonta a matsayin wacce za a iya tarawa da ita.

Sai dai wasu iyayen na ganin za su rika samun kudi idan suka yi wa 'ya'yansu kanana auren wuri.

Ƙananan amare na ganin yin aure zai ba su damar ci gaba da karatu. Amma ƴan matan kan ƙare ne a zaman gida bayan sun samu juna biyu ko kuma a barsu suna ayyukan gida.

Ba a cika kamawa ba da hukunta masu saɓa dokar ba kuma hukumomi da suka haɗa da ƴan siyasa ana zarginsu da kawar da idonsu kan abin da ya shafi harakokin addini wanda ke da matuƙar tasiri a siyasance.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga gwamnati ta ayyana auren kananan yara a matsayin laifi sannan ta kawo karshensa.