Koriya ta Arewa ta gargadi Amurka da Koriya ta Kudu kan rawar-daji

Kim Jong-un

Asalin hoton, AFP VIA GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Gwamnatin Kim Jong-un ta ce Koriya ta Kudu da Amurka za su dandana kudarsu

Koriya ta Arewa ta gargadi makwabciyarta Koriya ta Kudu da kuma Amurka, da cewa za su haddasa gagarumin tashin hankali na tsaro idan suka ci gaba da shirinsu na atisayen hadin-gwiwa na soji.

Wannan ita ce sanarwa ta biyu a cikin kwana biyu da gwamnatin Koriya ta Arewar ta fitar, wadda ke nuna gwamnatin na kara wannan barazana ne, kafin rawar-dajin kasashen biyu kawayen juna, abin da Koriya ta Arewar ke dauka a matsayin wani shiri na yaki.

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya ce kasarsa za ra shirya wa Amurka ko dai da yaki ko da tattaunawa

Asalin hoton, Inpho

Bayanan hoto, Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya ce kasarsa za ra shirya wa Amurka ko dai da yaki ko da tattaunawa

Gwamnatin Koriya ta Arewa ta gargadi makwabciyar tata Koriya ta Kudu da cewa muddin ta sake ta shiga wannan atisayen soji da Amurka, hakan zai iya bata duk wata dama ta farfado da dangantakar kasashen biyu, wadanda a hukumance har yanzu suna yaki ne, duk da kawo karshen rikicinsu a 1953.

To sai dai kuma duk da wannan gargadi, na Pyongyang, Seoul da Washington din ko gezau, domin dubban sojojin Koriya ta Kudun da kuma dakarun Amurka sun ci gaba da shirye-shiryensu na wannan atisaye na shekara-shekara da za su yi a mako mai zuwa.

Seoul's presidential office says the leaders of both Koreas are exchanging letters

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ofishin shugaban Koriya ta Kudu ya taba cewa shugabannin kasashen biyu makwabta na musayar wasiku

Kari a kan gargadin, a jiya, Kim Yo-jong, mai karfin fadi-aji, kanwar shugaban Koriya ta Arewar, Kim Jong-un ta bayyana shirin a matsayin butulci, wanda ta ce za a ga mummunan abin da zai biyo bayansa.

Bayan kalaman nata ne, kuma 'yan sa'o'i sai aka daina amsa kiran waya a layukan tarho na kar-ta-kwana, na tsakanin jami'an kasashen biyu, da aka rika yi daga Koriya ta Kudun zuwa ta Arewa, layukan da a kwanan nan aka dawo da amfani da su.

Kasashen biyu- Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu na tuntubar juna sau biyu a rana ta hanyar waya don kyautata alaka

Asalin hoton, HANDOUT

Bayanan hoto, Jami'an Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu na tuntubar juna sau biyu a rana ta hanyar waya don kyautata alaka

Kasashen biyu sukan tuntubi juna ne ta layukan wayar, sau biyu a rana. Amma bara a shekarar da ta gabata 2020, a watan Yuni sai Koriya ta Arewa ta katse layin wayar, bayan da dangantaka ta kara tsami sakamakon watsewar wani taron koli na zaman lafiya a tsakaninsu.

Bayan gargadin kanwar shugaban ne, sai kuma a yanzu wani babban jami'in gwamnatin Koriya ta Arewar, Kim Yong Chol ya biyo da gargadin kawayen biyu abokan gabar Pyongyang, da cewa sun yi zabi mai hadarin gaske, wanda kuma a dalilin hakan za su fuskanci gagarumar matsalar tsaro.