Jam'iyyar APC: Yau ake fara zaben shugabanninta na mazaɓu a faɗin Najeriya

APC

Asalin hoton, APC

Sabon rikici na sake kunno kai a jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya kan halarcin shugabancin riko na jam'iyyar na kasa karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe yayin da za a fara zabukan shugabannin jam'iyyar na mazabu da kananan hukumomi.

Rikicin ya yi kamari ne sakamakon hukuncin da Kotun Koli ta yanke a ranar Laraba kan zaben gwamnan Jihar Ondo, wanda ya nuna shakku kan sahihancin Kwamitin shirya zabukan karkashin Gwamna Buni.

Hukuncin ya yi watsi da karar da dan takarar jam'iyyar PDP, a zaben gwamnan jihar Ondo na shekarar 2020, Eyitayo Jegede ya shigar, yana kalunbalantar nasarar Rotimi Akeredolu, na APC.

Karamin Ministan Kwadago da ayyuka na Najeriya, Festus Keyamo, ya gargadi jam'iyyar game da kyale Gwamna Buni ya jagoranci wadannan zabuka.

Sai dai jam`iyyar APC ta sake jaddada cewa hukuncin da kotun kolin ta yanke a kan shara`ar dan takarar gwamna na jam`iyyar PDP a jihar Ondo da gwamna Rotimi Akeredolu na jam`iyyar APC bai shafi halalcin shugabannin riko na jam`iyyar APC na kasa ba, kuma ba zai shafi ayyukan da suke aiwatarwa ba.

Ga martanin kwamitin riƙo na APC ɗin

Bayanan sautiMartanin kwamitin riko na APC daga bakin Farfesa Tahir Mamman

Yayin da ake shirin fara wannan zabe dai, jam'iyyar ta ce ba za a yi shi a jihohi biyu na ƙasar ba, da suka hadar da Zamfara da Anambra, saboda dalilan samun sabbin mutanen da suka shiga jam'iyyar da ake son a ba wa damar kintsawa a jam'iyyar, don ganin sun shiga sahun shugabanci.

Baya ga haka kuma akwai jihohi da dama a kasar da ake kyautata zaton samun rikici a zaben na yau, saboda rikicin cikin gida da jam'iyyar ke fama da shi, inda ake tunanin bangarorin da ke rikici da juna kowa zai je ya yi nasa taron.

Abin jira a gani dai shi ne abun da zai biyo bayan zabukan na yau, la'akari da cewa su kansu jagororin jam'iyyar APCn wasu rahotanni sun ce suna fargabar cewa wasu daga cikin mambobin jam'iyyar za su kalubalanci zabukan a kotu ko da an gudanar.