Gwamnonin PDP sun soki Buhari kan 'mayar da fadar shugaban ƙasa hedikwatar APC'

Asalin hoton, Facebook/Senator Bala Mohammed
Gwamnonin jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya sun yi Allah-wadai da Shugaba Buhari kan abin da ta kira "mayar da Fadar Shugaban Ƙasa ta Villa matsayin sabuwar hedikwatar jam'iyyar APC", suna masu cewa "ta 'yan Najeriya ce".
Gwamnonin 14 sun bayyana matsayarsu ne cikin wata sanarwar bayan taro da suka gudanar a Jihar Bauchi da ke arewacin ƙasar ranar Litinin game da halin da dimokuraɗiyya ke ciki a Najeriya da kuma sauran batutuwa.
Mahalarta taron ƙarƙashin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sokoto, sun haɗa da Gwamnan Bauchi Bala Mohammed, da Gwamnan Abia Okezie Ikpeazu, da Udom Emmanuel na Akwa Ibom, da Douye Diri na Bayelsa, da Samuel Ortom na Benue.
Sauran su ne: Ifeanyi Okowa na Delta, Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu, Nyesom Wike na Rivers, Oluseyi Makinde na Oyo, Ahmadu Umaru Fintiri na Adamawa, Godwin Obaseki na Edo, Darius Ishaku na Taraba. Sai kuma Mataimakin Gwmanan Zamfara Mahdi Mohammed.
Baya ga maganar siyasa, gwamnonin sun bayyana matsaya kan sauran al'amuran da suka shafi ƙasa ciki har da matsalar tsaro. Ga biyar daga cikinsu:
'Ba mu amince da zaɓen 'yar tinƙe ba'

Asalin hoton, PDP
Shugabannin na PDP sun bayyana ƙarara cewa ba su amince da tsarin 'yar tinƙe ba a zaɓen fitar da gwani da gwamnati ke yunƙurin "tilasta wa jam'iyyu aiwatarwa" a cikin ƙudirin gyaran dokar zaɓe da ke gaban majalisa.
"Ganawar ta yi Allah-wadai da yunƙurin tallafa wa jam'iyyun siyasa tsarin zaɓen fitar da gwani na 'yar tinƙe a cikin Kundin Dokar Zaɓe," a cewarsu.
"Tsarin zai bayar da damar tafka maguɗi kamar yadda Shugaba Buhari ya samu ƙuri'a miliyan 15 a zaɓen fitar da gwani na APC a 2018 amma kuma ya samu miliyan 15 kacal a babban zaɓen 2019. PDP na ba da shawarar a ƙyale jam'iyyu su yanke hukunci kan ko suna son 'yar tinƙe ko kuma a'a."
'Ku yi rajista don ceto Najeriya'

Asalin hoton, Facebook/Senator Bala Mohammed
Kazalika, zauren gwamnonin ya umarci dukkan 'yan Najeriya da su "samar wa kansu makamin siyasa domin ceto Najeriya".
Suka ce: "Gwamnonin PDP na umartar dukkan 'yan Najeriya da su yi amfani da damar yin rajistar zaɓe da ake gudanarwa ta yadda za su samu makamin ceto Najeriya daga gwamnatin APC."
'Ba mu yarda da tilasta wa gwamnonin PDP ba'
Haka nan, jam'iyyar adawar ta zargi APC da bin "salo na rashin gaskiya" domin "tilasta wa" mambobinta su koma jam'iyyar mai mulki.
"Har wa yau, mun yi Allah-wadai da salo na rashin gaskiya da ake bi wajen tilasta wa gwamnonin PDP da sauran masu ruwa da tsaki don komawa APC, jam'iyyar da ta lalata tattalin arzikin Najeriya kuma ta mayar da ƙasar filin kashe-kashe da haifar da ƙunci da rashin iya mulki."
'Gwamnatin tarayya ta haɗa kai da gwamnonia samar da aikin yi'
A ɓangaren tattalin arziki, gwamnonin sun shawarci gwamnatin tarayya ƙarƙashin jam'iyyar APC da ta haɗa kai da gwamnonin jiha domin rage rashin ayyukan yi ga matasa.
"Muna jaddada cewa a dakatar da magnganu na fatar baki game da tsarin sauƙaƙa hanyoyin kasuwanci yayin da zuba jari daga ƙasashen waje ke ci gaba da raguwa saboda wahalar da kamfanonin da ke son zuba jari a Najeriya."
Jam'iyyar ta nemi gwamnatin tarayya ta ƙara azama wajen haɓaka ɓangaren fasaha da sauran fannoni don samar da ayyukan yi.
'Lokacin kawo ƙarshen 'yan fashin daji ya yi'
Da suke magana kan matsalolin tsaro da suka addabi Najeriya, gwamnonin sun ce "lokaci ya yi na kawo ƙarshen ayyukan 'yan fashi da masu garkuwa da mutane da 'yan ta'adda".
Kazalika sun bayar da shawarar cewa "a yi amfani da ƙarfin soja da hanyoyin gargajiya na warware rikici da fasahar tattara bayanan sirri da kuma siyasa don zaƙulo su [masu laifi]".
"Fashi da garkuwa da mutane da ta'addanci ba hanyar neman kuɗi ba ce kamar yadda APC ke faɗa, manyan laifuka ne ga Najeriya da ke lalata tattalin arzikinmu da ilimi da kuma rayuwar yaranmu."











