Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Harin bam ya kashe mutum 30 a wajen sayayyar sallah a Iraƙi
Jami'ai a Iraƙi sun ce an kashe mutum aƙalla 34 kana aka jikkata aƙalla 60 a wani harin bam a Bagadaza babban birnin kasar.
Bam ɗin ƙirar gida, ya fashe ne a kasuwar al-Wuhailat mai cunkoson jama'a a gundumar Sadr City inda Musulmai 'yan Shia suka fi rinjaye.
Mai yiwuwa fashewar ta rutsa da mutane ne da ke sayayya ta jajibirin babbar sallah.
Wannan shi ne harin bam mafi muni da ya faru a Baghdad cikin wata shida da suka gabata.
Kungiyar IS ta ce ita ce ta kai harin, inda ɗaya daga cikin mayaƙanta ya sanya rigar bam.
Akwai rahotanni da ke cewa mata da ƙananan yara na cikin wadanda lamarin ya rutsa da su, kana shaguna masu ɗan dama sun kama da wuta.
Gwamnatin Iraƙi ta ayyana nasara a yaƙin da take yi da mayaƙa masu ikirarin jihadi a ƙarshen 2007.
Sai dai ƙananan ƙungiyoyi marasa tasiri na ci gaba da tayar da ƙayar baya nan da can a cikin ƙasar.
IS ta ɗauki alhakin kai wani harin bam da mota da aka kai a watan Afrilu, wanda ya hallaka mutum huɗu a wata kasuwar da ke birnin Sadr, inda yanki ne da mabiya Shia suka fi rinjaye.
Ta kuma ɗauki alhakin kai wani harin a Dandalin Tayaran a watan Janairu da ya yi sanadin mutuwar mutum 32.
Wannan ne mafi munin hari da aka kai a ƙasar cikin shekara uku.
Wani mai magana da yawun Firayim-ministan Iraƙi Mustafa al-Kadhimi ya ce ya bayar da umarnin kama kwamandan 'yan sanda na yankin, kana an fara gudanar da bincike a yankin.