Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mohammed bin Salman: Me ya sa Biden ya sassauta wa Yariman Saudiyya kan kisan Khashoggi?
- Marubuci, Daga Frank Gardner
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC kan Tsaro
Kafin ya zama shugaban ƙasar Amurka, Joe Biden ya taɓa kiranta "wararriya" saboda rawar da ta taka a kisan gillar da aka yi wa ɗan jaridar Saudiyya Kamal Khashoggi.
A matsayinsa na shugaban ƙasa, a watan Fabrairu ya bayar da izinin sakin wani rahoton leƙen asirin Amurka da ya zargi Yarima Mai Jiran Gadon Masarautar Saudiyya Mohammed bin Salman.
MBS, kamar yadda aka fi saninsa, ya ƙi yarda da cewa yana da hannu a lamarin.
Amma a yanzu, ƙasa da wata shida da zamansa shugaban ƙasa, gwamnatin Biden ta yi wa ƙanin MBS, Mataimakin Ministan Tsaro, Yarima Khalid bin Salman, tarbar ban girma.
Wannan ita ce ziyara daga wani mutum mafi girma daga Saudiyya tun bayan kisan na Oktoban 2018.
"Mutanen Yarima MBS na cikin Masarautar Saudiyya sun zage damtse wajen dawo da martabar MBS da Saudiyyan kamar yadda take a da," a cewar Michael Stephens, wani jami'i na Cibiyar Bincike Kan Tsaro ta Royal United Service, Rusi da ke London.
Ya ƙara da cewa: "Kana masarautar ta dogara sosai kan damarmakin tattalin arziki, yayin da aka yi watsi da batun tsaron yankin wanda a baya ake ɗauka da muhimmanci."
To hakan na nufin ƙasashen yamma sun yafe wa MBS kenan?
Ba lallai hakan ba ne, kuma ba lallai ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam ba ne, ciki har da Majalisar Ɗinkin Duniya, wacce taKE ci gaba da kira kan a gudanar da bincike mai zaman kansa da ya haɗa da mutum mafi ƙarfin faɗa a ji a Saudiyya, wato MBS.
Jami'an Saudiyya 15 ne suka tafi Istanbul daga Riyadh a 2018 cikin jiragen gwamnati biyu, inda suka jira Khashoggi, wani fitaccen mai sukar Yarima Mai Jiran gadon.
Da sanya ƙafarsa a cikin ofishin jakadancin Saudiyyan, sai suka danne shi, suka shaƙe shi har ya mutu sannan suka yi gunduwa-gunduwa da gawarsa.
Gaskiya mai ɗaci
Yarima Khalid bin Salman, wanda kwanan nan aka yi maraba da shi a Amurka, shi ne jakadan Saudiyya a Washington a lokacin.
Da farkon lamarin ya yi watsi da batun cewa kisan gilla aka yi wa Khashoggi a cikin ƙaramin ofishin jakadancin Saudiyya a matsayin "tsagwaron ƙarya mara hujja."
A lokacin da Turkiyya ta bayyana wa duniya abin da ya faru a ofishin jakadancin Saudiyyan ta hanyar naɗar bayanai, hakan ya tilasta wa gwamnatin Saudiyya sauya matsaya.
Ta ɗora alhakin hakan ne kan "faruwar wata hantsaniya" sannan daga ta kama wasu ƙananan jami'ai da laifi bayan wata shari'a da aka gudanar cikin sirri.
Amma hukumar leƙen asiri ta Amurka CIA ta ce da bai kamata ma hakan ya faru ba tare da sanin MBS ɗin ba.
Amurka ta sanya takunkumi a kan fiye da jami'an Saudiyya 70 kan abin da ya shafi take haƙƙin ɗan adam kuma tun bayan faruwar lamarin, sai shugabannin ƙasashen Yamma suke ware yarima mai jiran gadon a bainar jama'a.
Sai dai duk da haka gwamnatocin ƙasashen Yamma na ci gaba da kallon Saudiyya a matsayin ƙawarsu, wata katanga ta kare faɗaɗar Iran, muhimmiyar abokiyar hulɗar kasuwanci, abokiyar cinikayya mai gwaɓi a kasuwancin makamai kuma wata ƙasa mai ƙarfi a fannin ƙasuwar man fetur ta duniya.
To a nan ainihin siyasar take aiki.
Wasu majiyoyi da suka san yarima mai jiran gadon sun ce, akwai tazara tsakanin matsayar jami'an gwamnatocin Yamma, yadda a fili suke nesanta kansu da MBS, da kuma gaskiya mai ɗaci ta alaƙar difilomasiyya da ke tsakaninsu da masarautar.
Wanda hakan ce ta sa, tamkar ƙiftawar ido, ɗan uwan MBS na ƙut da ƙut ya sanya ƙafarsa a manya-manyan ofisoshi a Washington a makon da ya gabata.
'Komai lokaci ne'
Cikin kwana biyu, Yarima Khalid bin Salman ya yi taruka da Sakataren Harkokin Waje na Amurka Anthony Blinken; da Mai bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro, Jake Sullivan; da Sakataren Tsaro Lloyd Austin; da kuma shugaban Rundunonin Tsaro, Janar Mark Milley.
Jerin sunayen kaɗai ya isa ya nuna irin muhimmancin da Amurka ke bai wa Saudiyya a matsayin ƙawarta, duk da cewa ba a sanar da ziyarar ta Yarima Khalid ko tsarin yadda za ta kasance ba.
An bijiro da batutuwa da dama don tattaunawa, da suka haɗa da yaƙin Yemen, inda Saudiyya ke ƙoƙarin tsame kanta bayan gazawa wajen yin nasara a kan mayaƙan Houthi da Iran ke goyon baya, waɗanda suka ƙwace mulki ba bisa ƙa'ida ba a shekarar 2014.
Batun makamashi da kasuwar man fetur, batun tsaro a yakin Kusurwar Afirka da kuma dawo da batun yarjejeniyar makamin nukiliya duk suna cikin abubuwan da za a tattauna a teburin.
An kuma ruwaito cewa a batutuwan har da Afghanistan, inda a yanzu dakarun Amurka suka janye sannan ake fargabar cewa samun ikon Taliban zai sa al-Qaeda ta sake gina daularta a can.
Jami'an difilomasiyya da suka san Saudiyya sosai sun ce a wasu lokutan ita ɗin ƙasa ce mai wuyar sha'ani wajen mu'amala.
Kasashen Yamma za su ci gaba da nuna shakku kan Yarima Mohammed bin Salman, mutumin da ke da ra'ayin kansa, tsawon rayuwarsa.
"Har yanzu hanya ba ta buɗewa MBS ba sosai," a cewar Michael Stephens na Rusi.
"Ana buƙatar lokaci sosai kafin ƙasashen Yamma su shirya sosai da Saudiyya. Amma dai ana samun ci gaba a abubuwa da dama sai dai mai yiwuwa lokaci ne kawai zai nuna lokacin da zai iya sake ziyartar ƙasashen."