Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matsalar tsaro a Najeriya: 'Masu garkuwa da mutane sun aurar da ƴaƴanmu mata da suka sace'
Iyayen daliban da aka sace a makarantar garin Yawuri da ke jihar Kebbi a arewa maso yammacin Najeriya sun koka game da tashin hankalin da suka tsinci kansu tun bayan sace 'ya'yan nasu.
A cewar iyayen yaran, masu garkuwar na turo masu hotunan bidiyo da ke nuna cewa tuni aka aurar da 'ya'yansu mata kuma lokaci zuwa lokaci suna kiran su domin su yi magana da yaransu.
Kusan mako biyu ke nan da aka yi garkuwa da daliban a lokacin da suke makaranta.
Daya daga cikin iyayen daliban ya shaida wa BBC cewa a duk lokacin da suka kira masu garkuwar, su kan fada musu cewa yaransu na cikin koshin lafiya.
Sai dai ya ce masu garkuwar suna sanar da su cewa ba da su suke son sasantawa ba illa gwamnati.
"Wani lokaci su kan je da yaro, idan ka yi sa a an je da yaronka yana da lambarka sai a yi magana, amma ni tun sanda aka kwashi yaran, ba a taba zuwa da yarona inda ake magana ba". in ji shi.
Ya kara da cewa tun bayan sace yaran, yara 10 ne aka kira iyayensu suka yi magana da daliban.
Ya ce iyayen daliban sun gudanar da wani taro inda suka je wajen gwamnatin jihar Kebbi, "gwamna ya nuna damuwarsa kuma ya ce za a dauki matakai a kai, yau wajen mako biyu ke nan amma ba mu kuma jin komai ba".
Ya kara da cewa suna cikin tashin hankali ganin yadda sallar layya take gabatowa, "gidan kowa ana murna, gidajenmu ga shi muna cikin damuwa da baƙin ciki".
Ya kuma sake kira ga gwamnati da ta taimaka musu wajen kubutar da yaransu daga hannun masu garkuwar.
Matsalar garkuwa da mutane na kara zama babbar barazana a Najeriya inda alkaluma ke nuna cewa an sace sama da dalibai 1,000 da malamansu a hare-hare daban-daban da masu garkuwa suka kai makarantunsu a fadin arewacin Najeriya tun daga watan Disamban da ya wuce.
Sai dai gwamnatin kasar na yawan ikirarin shawo kan lamarin.