Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
TB Joshua: Yadda dubban mutane suka halarci jana'izar Fasto TB Joshua a Lagos
Dubban masu zaman makoki ne suka halarci bikin binne Fasto TB Joshua a Cocin Synagogue, Church of All Nations (SCOAN) a yankin Ikotun na jihar Lagos.
Faston mai shekara 57 ya mutu ne a ranar 5 ga watan Yuni bayan wata gajeruwar rashin lafiya, in ji sanarwar cocin.
Mutane daga fadin duniya na martaba Temitope Balogun Joshua, kuma dubbun-dubatar mutane ne kan halarci wa'azi da addu'oinsa mako-mako.
Mai wa'azin, wanda ke da kwarjini ya yi fice ne a cikin karshen shekarar 1990 wadda ta zo daidai da lokacin shirin ''nuna mu'ujiza'' da limaman Kirista da dama suka gudanar a kafofin talabijin ta Najeriya.
Mujami'arsa ta yi ikirarin warkar da nau'ukan cututtuka daban-daban da suka hada da cutar HIV/Aids kuma ya ja hankulan mutane da dama daga fadin duniya.
Mabiyansa sun fi kiransa da suna ''Prophet" kuma ya mallaki tashar talabijin ta Kirista Emmanuel TV, kana yakan yi rangadi zuwa kasashen Afirka da Amurka da Birtaniya da yankin Kudancin Amurka.
Mista Joshua ya fito ne daga iyalai matalauta kuma kawunsa wanda Musulmi ne, shi ya rene shi, bayan mutuwar mahaifinsa Kirista.
- Ku karanta ƙarin bayani kan TB Joshua: TB Joshua: TB Joshua: Waiwaye kan rayuwar ɗan Najeriyar da ya zama fitaccen mai wa'azin Kiristoci a duniya
Sauran shahararrun limaman Kirista na Najeriya ba su halarci bikin binne shi ba, wanda ke nuni da irin dangantaka mai tsami da ke tsakaninsa da su.
Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) da Kungiyar Kiristoci Masu Mu'ujiza (PFN) sun sha bayyana shi a matsayin "mai sojan gona'' wanda ke cikin ''kungiyar matsafa'' da suka yi kutse a cikin addinin Kirista.
Daga karshe ya samu karbuwa daga babbar kungiyar Kiristoci
Daga Andrew Gift, na sashen BBC Pidgin, Ikotun
A wajen cocin, an saukar da tutocin kasashe da dama kasa. Yana da matukar wahala a iya gane ko tutocin na wakiltar kasashen da faston ya ziyarta a lokacin yana raye ne, amma kuma turakun da aka kafa sun miƙe zuwa tsawon fiye da kilomita daya.
Dubban masu zaman makokin da suka hallara shi ma ya nuna yadda TB Joshua ya shahara a kasashen duniya - mutane daga kasashen Bahamas, da Jamhuriyar Dominic da kuma Afirka Ta Kudu, inda ya fi samun tagomashi.
Mutanen kauyen Ikotun-Egbe, da ke wajen birnin Lagos inda cocin yake, sun yi fitar farin dango a ranar Alhamis don kallon wucewar motar daukar akwatin gawarsa, kuma da dama sun yi layi a kan titina da sanyin safiya a ranar Jumma'a.
Akasarinsu ba mambobin cocinsa bane amma sun amfana da irin taimakon da yake yi wa mutane. Da dama sun ci gajiya a kaikaice daga masana'antar da cocinsa mai cike da kai komo da kafa.
Manyan bakin da suka halarci jana'izar sun hada da gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu, jihar da Mista Joshua ya fito, wanda ya karanto wani sashen daga littafin Bible.
Ita ma Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), wacce ta yi takun-saƙa da TB Joshua a baya kan salonsa, ta aike da wakilai zuwa bikin binnewar na ranar Juma'a, da ke nuna cewa rashin jituwa ta ƙare.
Daya daga cikin abubuwan da ya so kenan a lokacin yana raye - ya samu karɓuwa daga kungiyar addinin Kirista mafi girma a Najeriya.
Muhimmin abu ne da hakan ta faru a lokacin mutuwarsa.
Matarsa Evelyn Joshua, wacce yanzu aka naɗa ta a matsayin babbar mai kula da cocin, ta ce marigayi mijinta ya bunƙasa cocin daga mai mambobi takwas zuwa yadda yake a yanzu.
"Kafin zinari ya zama zinari dole sai ya sha wuta. Ina son in gode maka kan kasancewa uban ƴaƴanmu,'' ta bayyana a ranar Talatar da shafe ana gudanar da addu'o'in yabo da girmamawa.
Ƴaƴansa su ne Sarah Joshua da Promise Joshua da kuma Heart Joshua, sun bayyana mahaifinsu a matsayin ''mutum mai ƙwazo da ƙarfafa gwiwa''.