Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Afirka na farfaɗo da wasanta na motsa jiki da ya shahara a Brazil
Brazil ta yi suna wajen wasan motsa jiki mai salon rawa, amma ainihin tushen wasan yana can tsallaken tekun Atilantika. A kasar Angola, wani mutum yana kokarin farfado da tsohon wasan domin tunawa da tarihin da aka manta da shi, kamar yadda marubuciya Marcia Veiga ta bayyana.
Sau uku a kowanne mako, cikin tsananin zafin rana Lucio Ngungi ke fitowa babbar farfajiyar gidan da ke babban birnin Angola wato Luanda.
A hankali yake gangarawa filin da ake wasan kwallon kwando, wanda a daidai lokacin da rana ke shirin faduwa yake cika makil, ga kuma sautin tafi rafrafraf da ake yi, hade da waka da kidan gangunan da mawaka ke yi.
Yana kewaye daliban da ke sanye da riga mai launin ruwan dorawa da aka yi wa ado da zanen gargajiya da launin baki, cikin zakuwar su fara atisaye.
Cikin tsanaki sai su fara jujjuyawa, kasa-kasa, su yi dama su yi hagu a wani salo da ake wa lakabi da Ginga.
Cikinsu akwai Ngungi, wanda ke sajewa da daliban suna waka da jujjuyawa: "Babu ragi, babu kari, wani ilimi ne na daban."
Wannan shi ne salon motsa jikin gargajiya na Angola, wanda ake yi a ko dai kasar Brazil ko ita Angolar kanta.
Sai dai ainihin sunan ya samo asali ne daruruwan shekaru da suka gabata, tun ma kafin a fara ciniki da safarar bayi daga kudancin Afirka zuwa kudancin Amurka.
A yanzu kasar Brazil ta gaje wasan ta hanyar yi masa kwaskwarima da wakoki da daɗaɗan kalamai a ciki, da ya sha kan wanda aka gada daga Afirka.
An rage tasirinsa a Afirka
Yanayin wasan na Angola na cike da shauki, kuma motsin da ake yi a tsanake ake yin sa, sannu a hankali ana yin kasa har a cimma kasa. Wannan ne dalilin da ya sa ake kidan a hankali, idan aka kwatanta da wanda ake yi a Brazil mai cike da kida.
Abin da ya bambanta wasannin biyu bai taka kara ya karya ba, inda dukka bangarorin biyu ke bukatar kida da waka, wanda ke sanya wa masu yi karsashi da shaukin yi ba tare da gajiyawa ko kosawa ba.
Butin Ngungi shi ne inganta wasan ta yadda zai sake yin suna a duniya. Kusan shekaru 20 kenan da ya fara atisaye a yankin Capoeira, amma bayan shekaru bakwai, sai ya samu labarin salon motsa jikin na Angola, nan da nan ya gane ba zai iya taka rawa a yankin ba.
"Ina yawan tambayar kaina, me ya sa zan ci gaba da atisaye a yankin, alhalin zan iya zuwa tushiyar abin a kasata?" in ji Ngungi mai shekara 36 a duniya.
Saboda rashin samun cikakkun bayanai, dole ya niki gari zuwa Brazil inda ya samu ganawa da Pedro Trindade - wanda aka fi sa ni da suna Mestre Moraes - wanda ya koyi salon motsa jikin a kasar Angola tun a shekarun 1980.
"Wasu lokutan na kan fusata, idan na tuna irin gudummawar da Angola ta bada ta fannin wasan amma aka mai da ta gefe tamkar ba ta yi komai ba," in ji Ngungi.
Mestre Moraes ya ce da gangan aka dakile tasirin Afirka a harkar, saboda wariyar launin fata.
"An amince wasan na daga cikin al'adun Afirka, aka kuma yi masa a ji a fannin cin zarafi saboda alakar shi da lokacin."
A tsakiyar karni na 16, a lokacin da bayi ke aikin gona, sun kirkiri salon motsa jikin da ya zamo na farko a Brazil, inda suke sanya salon fada a ciki amma ta hanyar wayancewa da salon rawa.
Bayan kawo karshen cinikin bayi a Brazil a shekarar 1888, gwamnati ta haramta wasan motsa jiki na capoeira, saboda tsoron hakan ka iya barazana ga bayin da aka 'yanta wajen mantawa da halin da suka tsinci kansu a ciki lokacin da ba su da 'yanci.
Amma an ci gaba da yi ta karkashin kasa, ba tare da gwamnati ta sa ni ba kuma shi ne ya kara farfado da wanda ake yi a kasar Angola.
A shekarar 930, Reis Machado, da aka fi sa ni da suna Mestre Bimba, ya samar da hanyar koyar da capoeira cikin sauki.
Bayan ciwo kan hukumomi kan muhimmancin al'adar, sai aka dage haramcin, aka kuma bude makarantar horas da mutane wasan motsa jiki na capoeira kuma ta farko a Brazil.
Sai dai duk da haka, ana yi wa wasan capoeira kallon hadarin kaji, musamman bayan Brazil ta fara koyar da shi a makaranta.
A matsayin maida martani, sai Mestre Bimba ya kafa sabon tsari, ta hanyar gabatar da fararen kayan makaranta ga dalibai, tare da koya musu yadda za su yi tsafta.
Wannan ya sanya wasan na, capoeira ya fara daukar hankalin duniya, aka fara amfani da shi a salon motsa jiki a sassan duniya.
Wannan shi ne silar fara wasan motsa jikin Capoeira na yanki.
Yayin da wasu ke ci gaba da bin tsohuwar hanyar motsa jikin, a bangare guda sun amince da yin amfani da sunan Capoeira Angola domin bambance su. Amma a hankali sai aka hade su duka biyu tare da mantawa da abin da ya faru a baya.
Sai dai wasan na Brazil ya fi na Angola bunkasa. Don haka Mestre Bimba ya fara amfani da sanya kida da waka wajen salon da ake kira tambourine.
'Fushin da nake yi ya ragu'
Duk da sunan da kuma ikirarin asalin wasan ya fito ne daga Angola, ana ci gaba da tababa kan hakan, duk kuwa da cewa bayin da aka yi safararsu zuwa Turai sun bi ta kudanci da tsakiyar Afirka.
Ana kuma danganta wasan da na al'adar 'yan Angola, da ake kira N'golo inda maza biyu ke takarar neman auren budurwa, za su yi wasan kokawa ta hanyar nuna kamar su na fada da Jakin dawa.
Koma dai yaya batun ya ke na usuli ko ta inda wasan ya samo asali, Ngungi ya zage damtse domin ganin ya farfado da al'adar da aka man ta da ita.
Ya na da shekara 15 ya tserewa yakin basasar Angola, amma tun bayan daowarsa kasar a shekarar 2014 ya ke kokarin kawo sauyi a kasar.
Ngungi ya zama ma'aikacin sa kai, shi ne ya fara bude makarantar koyon salon motsa jikin Capoeira ta farko a kasar mai suna, Escola de Capoeira Angola Okupandula, ma'ana "mu na godiya gare ku da kakannin mu".
An ba shi matsayi na musamman, kuma yana da karamar makaranta da tsirarun dalibai.
Kidan da ake yi da ganguna, da na sarewa da ake kira - agogô na karade baki dayan yankin, kuma tamkar mayen karfe kidan na karadawa ko'ina.
"Ina tsayawa a gaban gidana, ina kokarin gano ta inda kidan ke fitowa, sai kawai na hango Ngungi ya na tahowa," in ji dalibi Kelly, mai shekara 17.
Shi ma dalibi, Marcos, mai shekaru18, ya gano wasan motsa jiki na Capoeira ne ta hanyar jiyo kidan daga nesa shekaru biyar da suk wuce.
"Ina wasan motsa jiki na Capoeira na Angola kwanaki biyar a koanne mako, ina jin dadin yadda wasan ke cire min bacin rai, yana taimaka min cire gajiya da rage min damuwa, ya kuma sanya na manta matsalolin rayuwa.
Mafarkin Ngungi shi ne wata rana ya sayi makeken fili, ya gina katuwar makaranta da zai ci gaba da koyar da matasan Angola yadda za su yi amfani da wasan domin ci gaban al'ummarsu.
"Na damu matuka kan makomar al'ummarmu, ina yawan tunatar da kaina, hakki ya rataya a wuya na domin kawo wa al'umma ta ci gaba."