Hotunan yadda gurbacewar muhalli ke barazana ga tekunan duniya
Mai ɗaukar hoto Mandy Barker ta shafe sama da shekara 10 tana samar da hotuna na sharar teku domin wayar da kan al'umma game da girman yadda ake gurɓata tekunan duniya.

Asalin hoton, Mandy Barker
"Na fara ɗaukar hotunan tarkacen teku a shekarar 2009, lokacin da na lura cewa bakin tekun yankinmu na tattare da tarkacen shara na kayayyaki fiye da abin da hankali zai ɗauka," in ji ta.

Asalin hoton, Mandy Barker
An ƙiyasta cewa fiye da tan miliyan takwas na tarkacen kayayyakin roba ne ke mamaye tekunan duniya duk shekara.
Tarkacen na haifar da hadari mai yawa ga halittun ruwa.

Asalin hoton, Mandy Barker
Barker ta ɗauki hotunan abubuwan sharar tekun a tafiye-tafiye da ta yi zuwa zuwa gabar tekuna.

Asalin hoton, Mandy Barker
"Nakan fara ɗaukar hotunan abubuwa ƙanana, sannan sai matsakaita da manya-manya.
"Wadannan kuma sai a tsara su wuri ɗaya, wanda zai bayar da abubuwan."

Asalin hoton, Mandy Barker
An nuna ayyukan Barker a sassan duniya, kuma an yi amfani da su a binciken kimiyya da na ilimi.
Ba a daɗe ba aka gayyace ta don ta yi jawabi game da batun a ranar buɗe taron Tarayyar Turai na sauyin yanayi na Greenweek 2021 ba.
"Ta hanyar aiki da masanan kimiyya, zan iya gabatar da bincikensu ta hanyar fasaha - kusan bai wa kimiyya "murya a bayyane" - domin jan hankalin mutane su karanta game da batun," in ji ta.

Asalin hoton, Mandy Barker
"Wayar da kan mutane game da gurɓatar teku wani abu ne da a yanzu na sadaukar da rayuwata a kai.
"Ina da burin na bayyana illar da ke tattare da rayuwar halittun ruwa a teku da kuma mu kanmu, daga ƙarshe hakan ya sa mai kallo daukar mataki."

Asalin hoton, Mandy Barker
Yanzu haka ana baje-kolin aikin Mandy Barker a matsayin wani ɓangare na bikin baje-kolin hotuna na Belfast a Donegall Quay, Belfast, har zuwa 30 ga Yuli 2021.











