Cryptocurrency: Makarantar da ta fara karɓar kuɗin intanet a matsayin kuɗin makaranta a Kano

Wata makaranta mai zaman kanta a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta fara karɓar kuɗin intanet na cryptocurrency a matsayin kuɗin makarantar da ɗalibai za su dinga biya.

Shugaban makarantar, Sabi'u Musa, ya shaida wa BBC Hausa cewa ya ɗauki wannan mataki ne don ganin yadda kuɗin intanet yake ta samun ƙarin karɓuwa a duniya.

A ranar Alhamis ne Malam Sabi'u ya fara shaida wa manema labarai wannan mataki nasa da wadda makarantar New Oxford Science Academy da ke unguwar Chiranchi ta ɗauka.

Ya ƙara da cewa hukumar makarantar ba ta ɗauki matakin ba sai da ta tuntuɓi iyayen yara don jin ta bakinsu.

"A haƙiƙanin gaskiya mun fito da wannan tsari ne ganin yadda duniya ke ta tururuwa wajen amfani da kuɗin intanet," a cewarsa.

"Kuma Alhamdulillah yanzu idan kuka duba ƙasashe irin su El-Salvador sun halatta cryptocurrency ya zama kuɗin kashewa a ƙasar.

"Duba da irin wannan ci gaba da kuma hasashen da masana ke yi, na tabbata nan da shekaru kaɗan cyrptocurrency zai mamaye harkar kuɗaɗe a duniya," in ji shi.

Malamin ya ce hakan ce ta sa ya ga irin wannan ci gaba bai kamata a bar ƙasa irin Najeriya a baya ba, "duk da dai ƙasarmu mai tasowa ce amma ya kamata a tafi da mu a wannan tsarin don ƙasashen da suka ci gaba ma sun saka ɗamba."

Ya ce ya ga kamatar ya shiga cikin tsarin tun a farko-farkonsa kafin lokaci ya ƙure, ya zama damar ba ta da yawa.

Wasu labaran da za ku so ku karanta

'Ba tilas ba ne'

Amma ya jaddada cewa ba a wajabta biyan kuɗin makaranta da cryptocurrency ba, zaɓi ne ga iyayen da suka ga suna da buƙatar hakan, waɗanda ba su da buƙata kuma sai su biya yadda suka saba.

"Tuni muka samu hadin kan da yawa daga iyayen yaran, don ko a jiya ma wasu sun zo sun biya da Dutch coin, ka ga wannan ci gaba ne sosai.

"Wani daga cikin iyayen ma farin ciki ya bayyana ƙarara da wannan mataki. Saboda ya ce a yanzu dama ana cikin hali na rashin kudi a ƙasar, to sai ga wannan zaɓin, da ma kuma yana da coins (silalla ko kuɗin intanet) ɗin a ajiye.

"Shi kenan sai ya ga ai faɗuwa ta zo daidai da zama."

Malam Sabi'u ya ce suna bayar da adireshin asusun makarantar na intanet wato wallet sai mutum ya tura coins ɗin ta intanet.

Harkar dai ba ta amfani da kuɗi laƙadan ba ce, harka ce da ake tura komai ta intanet.

Malamin ya byayana farin cikinsa da jin dadinsa kan yadda lamarin ya fara samun karɓuwa da kuma fatan abin zai ci gaba da samun tagomashi.

Sai dai a yayin da wannan makaranta ta fito da wannan sabon tsari, shi kuma Babban Bankin Najeriya (CBN) a watan Fabarairun 2021 ya fitar da sanarwar dakatar da amfani da kuɗin na intanet da dangoginsa sannan ya umarci bankuna su rufe duk wasu asusu da ke aiki da kuɗin.

Ita ma hukumar da ke kula da hannayen jari a Najeriya, SEC wacce a baya ta taɓa nuna a shirye take ta amince da kuɗin intanet, ta goyi bayan matakin na CBN.

Ta ce ba za ta amince da shi ba a yanzu har sai tsarin bankunan Najeriya ya samar da hanyar amfani da kuɗin inatent yadda ya kamata - kamar dai yadda CBN ya ce.

Karin labarai masu alaƙa