Mummunar illar da gwajin makamai masu linzami ke yi wa halittu a teku

Asalin hoton, US Navy
A cikin hoton, wata babbar da'ira da ke tekun ta koma fara fat kana igiyar ruwa mai karfi na karkada na'urar daukar hoton.
Sannan wani makeken fushin ruwan teku ya yi toroƙo zuwa ƙololuwar sama, kana ya sake makowa zuwa kasa. Daga nesa, wani babban jirgin ruwan yaki ya bayyana a yayin da na'urar daukar hoton take kewayawa.
A ranar Juma'ar da ta gabata, rundunar sojin ruwan Amurka ta yi gwajin yadda sabon jirgin ruwan yaƙi ƙirar zamani da ke daukar jirgin sama, USS Gerald R. Ford zai iya jure wa duk wata fashewa da ta faru a kusa.
Yana amfani da kusan tan 18 na ababen fashewa - da girmansa ya ninka girman abin da ake kira "Mother of All Bombs" (MOAB), makamin nukiliya mafi girma a rumbun ajiyar makamai na Amurka.
Fashewar mai girman gaske ce da har sai da hukumar safiyon kimiyyar kasa ta yi rijistarsa kan karfin ma'aunin girgizar kasa 3.9, kuma bayan da aka yada hoton a ko ina, ya yi ta samun tagomashi a shafukan sada zumunta cikin wannan makon.
"Mene ne takamaimen abin da girman wannan fashewa ke yi wa rayuwar cikin teku ?" Mutane suka tambaya.

Asalin hoton, US Navy
"Muddin wata fashewa ta kasance mafi girman da za ta lalata jirgin yaƙi, ko shakka babu za ta iya yin ta'annati ga halittun da ke cikin teku,'' in ji editan sashen kimiyya na BBC David Shukman.
"Masunta kan yi amfani da nakiya wajen kashe kifaye - don haka mun san cewa ababen fashewa na da hadarin gaske ga halittun ruwa. Kuma babbar fashewa za ta hallaka da daman su.''
Michael Jasny, Daraktan kare halittun ruwa na kungiya mai zaman kanta ta Natural Resources Defense Council, ya amince da wannan ra'ayi.
Ya shaida wa BBC "wasu kananan halittun ruwa da ke kilomita daya zuwa biyu tsakaninsu da wurin fashewar za su iya hallaka, kuma wasu da ke kusan kilomita 10 za su iya samun munanan raunuka na dindindin da suka hada da matsalar ji.''
Lalacewar kunne babbar matsala ce ga halittun ruwa.
"Sautin igiyar ruwan kasan teku na iya tafiya mai nisa kuma dabbobin ruwa na whales na amfani da hakan wajen ganowa ko jin abubuwa daga nisan mil dari,'' in ji Shukman.
"Don haka ka yi tunani yadda wannan karfin girgiza da ke haddasa babbar kara daga fashewar zai shafi ji."

Asalin hoton, Getty Images
Dabbobin ruwa kwararru ne wajen nutso da ninkaya - ga misali dabobin whales masu bakin kifi, kan yi nutso na tsawon mita 2,000 a karkashin teku.
Haske kan dusashe a karkashin teku cikin sauri, kuma da tsawon kilomita a can kasa nan ne inda duhu kan fara.
A wadannan wurare masu zurfi, dabbobin na whales na dogara ne da sauti wajen kai komo, wanda shi ya sa masana kimiyya suka ce kurman whale tamkar mataccen whale ne.
Girgiza
Tayar da ababen fashewa a karkashin teku na haifar da girgizar teku da kuma rikirkita yanayin karfin motsawar teku, kana akwai abubuwa da dama da suka faru da kuma yi nakasu ga rayuwar dabbobin ruwa da daman gaske.
Dabbobin ruwa na porpoises masu kama da whales da dama ne suka kurumce da kuma mutuwa a cikin watan Agustan shekarar 2019, bayan da aka yi amfani da ababen fashewa a tekun Baltic don lalata nakiyoyin da aka dasa a lokaci yakin duniya na biyu.
Shekaru 10 da suka gabata ne a yankin Scotland, wasu dabbobin ruwa na whales masu fuka-fukai da ke da tsawon mita 39 suka makale a gefen teku a kan wata doguwar igiyar ruwa, inda daga bisani 19 daga cikin su suka mutu.
Wani rahoton gwamnatin Birtaniya ya gano cewa wasu ayyukan lalata bama-bamai da aka yi a kusa a cikin kwanakin ne suka haddasa wannan mummunan abu.

Asalin hoton, Getty Images
A shekarar 2013, ita kanta Rundunar Sojin Ruwan Amurka ta amince cewa wannan horo da kuma gwaji ka iya hallaka daruruwan dabobin ruwa na whales da dolphins, tare da jikkata dubbai nan da karin wasu shekaru biyar, akasari saboda fashewar karkashin kasa.
Girma na da amfani
Amma duk da cewa muna da misalai da dama na dabbobin da lamarin ya shafa a tsakanin manya halittun ruwan, yana da matukar wahala a iya ƙididdige ta'annatin da hakan ya yi wa kananan halittun ruwan, duk da cewa akwai yiwuwar su suka fi fuskantar hadarin.
Peter Ward, wani ƙwararre ne a fannin al'amuran da suka shafi karkashin teku da halittun da ke ciki wanda ya yi nazari a fannin tasirin ababan fashewa a karkashin teku kuma ya rubuta wata kasida a shekarar a 2015.
A binciken da ya gudanar, ya yi nuni da mummunan tasirin da nakiyoyin da aka dasa cikin teku za su iya haifarwa.
''Nakiyoyin da aka dasa a cikin teku na ƙunshe da ababan fashewa masu karfin gaske da ke da nauyin kilo 450 zuwa 680, kuma suna haddasa asarar rayukan halittun ruwa da ke da nisan mita 300 zuwa 630 daga wurin," in ji shi.
Amma kuma, ya yi nuni da cewa ''girman dabba shi yake nuna yanayin girma damar tsira daga fashewar.''











