Sauya mana matsuguni a Ibadan ya jawo mana asarar N5m - Mabarata

mabarata

Asalin hoton, Getty Images

Gwamnatin jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya ta sauya wa almajirai da naƙasassu wajen zama daga Unguwar Sabo zuwa Akinyele can wajen birnin Ibadan.

A wata sanarwa da gwamnatin jihar ta raba wa manema labarai ta ce sauya wa naƙasassun matsugunni ya zama dole don bai wa gwamnati damar inganta kula da su da muhallansu.

Sai dai mabaratan sun koka da cewa kwasar gaggawa da jami'an gwamnatin suka yi musu ba tare da takardar gargaɗi ta janyo suka yi hasara ta miliyan biyar zuwa shida a unguwar ta Sabo-Ibadan.

Tuni dai naƙasassun, waɗanda suka haɗa da makafi da guragu da mabarata da sauran masu fama da lalurar jiki da ba za su iya wani aikin ƙarfi ba ne aka sauya wa matsugunnin.

Tsohon yankin da suke a unguwar Sabo, wani yanki ne da al'ummar Hausawa suke da ƙarfi da yawa; zuwa yankin Akinyelen, wani waje da yake da nisa da Ibadan babban birnin jihar.

Naƙasassun da sauran mabarata sun bayyana cewa sauya musu matsugunni ba tare da tuntuɓarsu ya sa su cikin takura a yanayin da suke da iyalai, kana kuma aka kai su unguwar da ba su shirya mata ba.

Mabaratan da ke da ƙananan sana'oi a bakin Sabo sun bayyana cewa sun yi asarar dukiya ta miliyoyin naira sakamakon rashin barin su su tsira da komai.

Sarkin Makafi Ibrahim Muhammad ya ce yankin da aka mayar da su takurarre ne ga mai iyali, kana kuma kafin a mayar da su Akinyele babu wani jami'in gwamnati da ya aika musu takardar gargaɗi kafin a umarci su bar unguwar Sabo.

"Jiya aka aika mana kuma a jiyan aka ce mu bar wajen. Mun nemi alfarma aka ƙi yi mana. Haka suka kwashe mu ko kayayyakinmu ba mu ɗauka ba. Amma tun da hukuncin gwamnati ne yaya za mu yi?

"A taƙaice mun yi asara ta kai ta miliyan shida ko biyar," in ji shi.

Malam Mustapha Umar shi ne sarkin guragu na jihar Oyo ya ce: "An tauye mana haƙƙi sosai, ba a ba mu notis ba. To shi mnenan don muna naƙasassu sai a tauye mana ƴanci, ana mana abubuwa kamar mahaukata," a cewarsa.

Ya kuma ce abin da gwamnatin jihar Oyo ta aiwatar zai jefa su a mawuyacin hali.

A yanzu dai mabaratan sun ce suuna da buƙatu da dama sa suke so gwamnatin jihar Oyo ta yi musu domin ci gaba da jure zama a sabon yankin na Akinyele.

Wannan layi ne

Me gwamnatin Oyo ta ce?

mabarata

Asalin hoton, Getty Images

A wata sanarwa da sakataren watsa labarai na gwamnan jihar, Taiwo Adisa ya fitar ta ce gwamnatin Jihar Oyo ta fara aikin kwashe mabarata daga kananan hukumomi da birnin Ibadan zuwa sabon matsugunnin su dake a Akinyele.

Sanarwar ta kara da cewa tsarin kwashe mabarata daga tun ba yau ba aka cimma matsayar tayar da su daga unguwar Sabo, to amma sai a ranar Talatar da ta gabata aka fara aikin wurjanjan.

Gwamnatin jihar Oyo ta ce kafin a mayar da mabaratan zuwa Akinyele sai da aka masu fada a ji na al'ummar arewa da ke a jihar da wakilansu suka kai ziyara sabon matsugunnin kafin daukar mataki da mabaratan ke ƙorafi a kai.

Taiwo Adisa, babban sakataren watsa labarai na gwamnan jihar Oyo a cikin sanarwar da ya raba wa manema labarai ya bayyana cewa da masaniyar kwamishinan muhalli da wani lauya Barista Idowu Oyeleke ne suka jagoranci rukunin farko na mabarata zuwa sabon matsugunnin nasu.

Ta kara da cewa an samar da abubuwan more rayuwa da suka hada da makarantu da asibitoci da kuma wuraren shaƙatawa.

Wani lokaci a baya wasu mutane sun yi zargin wasu daga cikin mabaratan da ake ba su sadaka da amfani da kudaden da suke samu domin aiwatar da ƙulunboto ko wani abu domin wata buƙata ta bil'adama, inda hankali wasu daga mazauna jihar ya tashi.

To amma mabaratan sun musanta hakan, inda har taron manema labarai suka kira.

Idan dai ana iya tunawa cikin watan Oktobar shekara ta 2019, gwamnatin jihar Oyo wanda gwamna Seyi Makinde yake jagoranta ta fara aikin sauyawa mabaratan matsugunni da a baya ta ce suna zaune a kan titunanan jihar "kuma hakan hadari ne da lafiyarsu da ta iyalansu."

Wannan layi ne