Israel ta kai wa Gaza hari bayan martanin Hamas da balan-balan
Isra'ila ta ce ta kai hare-hare ta sama bayan da Hamas ta harba wasu abubuwa masu fashewa daga Zirin Gaza. Wannan martani ne domin abubuwan fashewan sun tayar da gobara a wasu yankunan Israel a sanadin balan-balan ɗin da Hamas ta harba daga cikin yankin nasu.
An ji ƙarar fashewar abubuwa a birnin Gaza da sanyin safiyar Laraba.
Hamasa ta aika da gomman balan-balan zuwa cikin IIsera'ila ne ranar Talata wanda ya janyo gobara na tashi a wurare- masu dama, kamar yadda hukumar kashe gobara ta Isra'ila ta sanar.
Wannan ne rikicin farko tsakanin Isra'ila da Hamas tun da a ka tsagaita wuta ran 21 ga watan Mayu.
Matakin ya biyo bayan wani maci da Yahudawa masu tsanannin kishin ƙasa su ka yi a yankin gabashin birnin Qudus a ranar Talatar, wanda ya aifar da kakkausar suka daga Hamas, wadda ita ce kungiyar da ke gudanar da yankin na Gaza a hukumance.

Asalin hoton, Getty Images
Abin da aka sani game da wannan rikicin
Wata sanarwa da rundunar tsaron Isra'ila IDF ta fitar, ta ce jiragen yakinta sun kai hare-hare kan wasu gine-gine na rundunar da ke kare yankin Khan Yunis a cikin birnin Gaza.
Ta kuma ce "ayyukan ta'addanci" na aukuwa a wadannan wuraren, kuma rundunar "a shirye ta ke ta tukari dukkan martanin da zai byo baya, wadanda su ka hada da ci gaba da kai hari a Zirin Gaza".
Sai dai ba a tabbatar ko akwai wadanda wannan harin ya jikkata ba.
Wani kakakin Hamas ya fitar da wata sanarwa a Twitter yana cewa Falasdinawa za su ci gaba da "jajircewar da su ke yi da kare 'yancinsu da yankuna masu tsarki" a birnin Qudus.
Hukumar kashe gobara ta Isra'ila ta ce balan-balan din da mayakan Hamas su ka harba sun haifar da gobara kimanin 20 a wasu yankunan kudancin Isra'ila.












