Da gaske jiragen sojin Najeriya sun halaka shanu 1,000 a Nasarawa?

Asalin hoton, Getty Images
Wasu rahotanni sun bayyana cewa wani jirgin sojin Najeriya ya halaka shanu sama da 1,000 a wasu jerin hare-hare kan matsugunan Fulani makiyaya a yankunan ƙananan hukumomin Keana da Doma na jihar Nasarawa a yankin tsakiyar Najeriya.
Sai dai Daraktan hulɗa da jama'a na rundunar sojin sama ta Najeriya Air Commodore Edward Gabkwet, ya shaida wa BBC cewa batun ba haka yake ba, babu ko saniya ɗaya da aka kashe a lokacin aikin sojin.
Amma shugaban kungiyar Fulani Makiyaya ta kasa Muhammad Kiruwa Ardon Zuru, ya gaya wa BBC cewa jirgin sojojin saman Najeriyar ya ƙaddamar da hare-haren ne a tsakanin ranakun Alhamis 10 ga watan Yuni da Lahadi 13 ga watan Yuni.
"Mun samu labarin kashe shanun daga jama'armu da ke waɗannan yankunan a lokacin da jiragen yaƙin sojin suka shafe kwanaki huɗu suna kai hare-hare a yankin,'' in ji shi.
Ardon Zurun ya kara da cewa ba a samu asarar rayukan mutane ba amma kuma hare-haren sun hallaka tare da jikkata wasu shanun a yankunan.
"Yanzu haka muna jiran cikakkun rahotanni daga shugabannin yankunan da za mu tantance mu tura wa shugaban kwamitin amintattu wato Sarkin Musulmi cewa ga abin da ke faruwa, domin a tura wa shugabannin sojojin," in ji shi.
Air Commodore Gabkwet ya ce, ''A lokacin da muka fara gudanar da ayyukan sojin a yankin, mun hangi wasu 'yan fashin daji dauke da makamai, da suka tsinkayi jirgin sojojin ya tunkari inda suke sai suka arce.
"Wasu suka shiga cikin daji yayin da wasu suka shiga cikin ƙauyuka, daga nan jirgin ya juya ya sake komawa sansanin soji, abin da ya faru kenan'' a cewar Mista Gabkwet.
Ya kuma ƙara da cewa; "Ta yaya za a ce an kashe shanu sama da dubu daya?
"Sai da na kira kwamishinan yada labarai na jihar Nasarawa na tambaye shi ta yaya har za a ce an hallaka shanu masu yawa irin wannan amma ba mu sani ba, shi ma abin ya ba shi mamaki!''
Sai dai kuma shugaban kungiyar Fulani makiyayan ta Miyetti Allah Muhammadu Kiruwa Ardo Zuru ya ce idan har sojoji sun musanta zargin kai wadannan hare-hare da kisan shanun, ya kamata su zo a zauna a bisa teburin shawara domin a fahimci gaskiyar maganar.
Jihar Nasarawa na daga cikin jihohin Najeriya da ake yawan samun hare-haren ƴan bindiga da rikice-rikicen manoma da makiyaya.
A baya-bayan nan ma an samu raotanni cewa mayaƙan Boko Haram sun yi sansani ta wuraren yankin.
Rikice-rikice da ke da nasaba da satar mutane don kuɗin fansa da kai hare-hare kan al'ummomi musamman na karkara na ƙara yawaita a sassan ƙasar daba-daban.
Ko a ranar Litinin sai da rahotanni daga tsakiyar Najeriya na suka ce ana fargabar kashe gommai a jihohin Filato da Benue.
A tagwayen hare-haren da aka kai jihar Benue an kashe mutum 11 a ranar 13 ga watan Yuni bayan wani ƙazamin hari kwana guda kafin nan.
Jaridar ThisDay ta ruwaito cewa an kona mutun shida da ransu a jahar Anambra, yayin da aka kashe karin wasu mutun 20 a jihar Filato.
Sai dai duk da wannan rashin tsaro da ke ci gaba da ta'azzara a Najeriya, Shugaban Buhari a wata hira da gidajen talabijin ya ce nakasun da gwamnatinsa ke samu wurin tunkarar matsalar tsaro na da alaƙa da rashin damar shigowa da isassun makamai.












