Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hajj 2021: Mazauna Saudiyya ne kaɗai za su yi aikin Hajjin bana
Hukumomi a Saudiyya sun ce jumillar mutum 60,000 ne kacal aka yarda su gudanar da aikin Hajji na bana, a cewar shafin Haramain Sharifain mai bayar da bayanai daga masallatan Harami biyu.
Kazalika, mazauna Saudiyya ne kaɗai za su gudanar da aikin na shekarar Hijira ta 1442, waɗanda suka ƙunshi 'yan ƙasa da kuma baƙi.
Shafin ya ce an ɗauki matakin ne sakamakon yaɗuwar sababbin nau'uin cutar ta korona a ƙasashen duniya.
Haka nan, rukunin mahajjata guda uku ne kaɗai za a bai wa damar yin ibadar. Su ne:
- Wanda aka yi wa rigakafin korona
- Wanda aka yi wa rigakafi guda ɗaya kuma ya shafe kwana 14
- Wanda aka aka yi wa rigakafi amma bai gama warkewa ba
Yadda cutar korona ta sauya tsarin gudanar da ɗawafi
Ɓullar cutar korona a faɗin duniya ta sa dole an sauya yadda ake gudanar da abubuwa da dama na yau da kullum ciki kuwa har da ayyukan ibada - kamar sallah cikin jam'i da daidaita sahu a sallar da ma yadda ake ayyukan Hajji da Umra kamar shi ɗawafin da safa da marwa da dai sauransu.
Da yake ɗawafi na ɗaya daga cikin manyan ayyukan Umrah da Hajji, hukumomin Saudiyya sun samar da hanyoyin yin sa yadda ba za a saɓa dokokin cutar korona ba.
A yanzu an sanya alama a ƙasan filin ɗawafi don nuna wa masu ɗawafi yawan tazarar da ya kamata su bari a tsakaninsu.
Kamar yadda aka saba dama, akwai ƴan sanda ko jami'an masallaci da ke shawagi a filin ɗawafi tun kafin zuwan cutar korona amma a masallacin Ka'aba yanzu, akwai jami'an masallaci na musamman da ke sa ido domin tabbatar da cewa maniyyata sun bar tazarar da ya kamata wato ba su cunkushe a wuri guda kamar yadda aka sani ba.
Dama kuma akwai iya adadin mutane da ake bari su shiga masallacin a lokaci guda ta hanyar amfani da wata manhaja don haka zai yi wuya a samu cunkoson mutane.
Sannan duk da tazarar da ake bari, dole ne mai yin ɗawafi ya sanya takunkumin fuska har ya fita daga masallaci.
Haka kuma, ba kamar yadda aka saba ba yanzu masu sanye da Ihrami ne kawai ake bari su shiga filin ɗawafi, amma su ma ba a bari su je kusa da Ka'aba.
An kewaye Ka'abar da wasu robobi da za su hana mutane wucewa su je kusa da ita.
Don haka babu taɓa Ka'aba da Hajrul Aswad da tsayuwa a ƙarƙashin indararon rahama kamar yadda aka saba.