Magawa gwarzon ɓera ya yi ritaya daga aikinsa na gano abubuwan fashewa

Magawa

Asalin hoton, Apopo

Bayanan hoto, An ce Magawa ya fara rage zafin nama saboda shekarunsa

Ɓeran mai suna Magawa, wanda aka yi wa kyautar zinare saboda bajintarsa, zai yi ritaya daga aikinsa na gano bama-bamai.

Cikin shekara biyar da ya kwashe yana aiki, ya sansano nakiyoyi 71 da gwamman abubuwan fashewa a tsawon rayuwarsa ta aiki a Cambodia.

Amma mai lura da shi Malen ya ce ɓeran dan asalin Afrika mai shekara bakwai "ya fara rage kuzari" saboda shekaru da suka fara masa yawa, dan haka akwai bukatar girmama sa.

An yi ƙiyasin cewa akwai nakiyoyi kusan miliyan shida binne a cikin kasa a Kudu maso Gabashin Cambodia.

Wata kungiyar kasar Belgium mai suna Apopo ce ta horas da ɓeran mai shekara bakwai, wanda dan asalin kasar Tanzaniya ne.

Ƙungiyar tana horas da dabbobi domin gano abubuwan fashewa da aka binne a karkashin kasa da kuma masu dauke da cutar tarin fuka a shekarun 1990, a kan bai wa dabbobi lambar yabo bayan sun samu horo.

A makon jiya, Apopo ta ce wani sabon rukunin matasan beraye ya gama karbar atisaye a Cambodia karkashin cibiyar (CMAC) sun kuma fita da sakamako mai kyau.

Malen and Magawa

Asalin hoton, Apopo

Bayanan hoto, Malen, wacce take kula da Magawa ta ce tana son biya masa dukkan buƙatunsa

Kungiyar ta ce Magawa zai ci gaba da zama a sansaninsu na 'yan makonni domin bayar da horo ga sabbin shiga.

"Lamarin Magawa na da birgewa, kuma ni abin alfahari na ne da na yi aiki da shi," in ji Malen.

"Dan karami ne amma ya ceci rayukan dubban mutane wanda hakan ya bamu damar kara bukatar aminci."

A watan Satumbar bara, Magawa ya sami kyautar PDSA ta zinare - a wasu lokutan ana kiransa da George Cross na dabbobi - saboda aikinsa na ceton rayuwa da yawa".

Shi ne bera na farko da ya fara karbar kyautar a cikin shekara 77 a tarihi.

Yana da tsayin 28 inci sai nauyin 1,2 kilogiram. Duk da cewa yana da tsayi sama da sauran beraye, Magawa ya yi kankanta ya tashi bam idan yana tafiya a gefensu.

An horas da berayen su rika gano abin fashewa, hakan na nufin suna kaucewa karfunan da ba su da hadari su nemi masu hadari cikin gaggawa.