Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
IPOB: Kalaman Buhari kan masu tayar da hankali a yankin ƙabilar Igbo sun jawo zazzafar muhawara
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce a kullum yana karɓar rahotannin hare-haren da ake kai wa cibiyoyin gwamnati yana mai cewa a bayyane yake cewa masu aikata hakan na son ganin gazawar gwamnatinsa ne.
Yayin da yake ganawa da jami'an hukumar zaɓe ta INEC a Abuja ranar Talata, Buhari ya ce matasan yanzu ba su san bala'in yaƙin basasa ba wanda aka yi a ƙasar daga shekarar 1967 zuwa 1970, har ma ya yi alƙawarin ɗaukar mummunan mataki a kan masu kai hare-haren.
A cewarsa: "Duk masu son lalata tsarin gwamnati za su sha mamaki kwanan nan. Mun ba su isasshen lokaci...Mu da muka shafe wata 30 a fagen daga, muka ga bala'in yaƙin, za mu bi da su da salon da suka fi ganewa."
Sai dai waɗannan kalamai nasa ba su yi wa wasu daɗi ba, suna masu cewa a matsayinsa na shugaban ƙasa bai dace ya yi kalaman da suka yi kama da na tashin hankali ba.
A gefe guda kuma wasu na ganin wannan shi ne abin da ya dace tuntuni shugaban ya yi.
Abin da 'yan Najeriya ke cewa
Tun bayan yin kalaman nasa da misalin ƙarfe 5:30 na yamnmacin Talata a shafinsa na Twitter, sunan Buhari kawai ake gani a saman dandalin shafukan zumunta saboda yawan muhawara da maratni iri-iri da bayanan suka jawo.
An yi amfani da kalmar 'Buhari' sau fiye da 189,000 a Twitter ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.
Kazalika ana muhawarar ce da sauran kalmomi irinsu 'Boko Haram' da 'Genocide' wadda ke nufin kisan kiyashi, da 'civil war' wadda ke nufin yaƙin basasa, da 'Igbo' wato ƙabilar Ibo mazauna kudu maso gabashin Najeriya.
"Yaƙin basasar da ya kashe mutum kusan miliyan uku shekara 50 da suka wuce, da shi Buhari ke yi wa 'yan kudu maso gabas barazana a 2021 yayin da ake gyara halin 'yan Boko Haram kuma 'yan fashin daji ke kashe mutane. Abin mamaki," kamar yadda wani mai suna Uncle Ajala (@UNCLE_AJALA) ya wallafa a Twitter.
Shi kuma Adamu Hayatu (@AHayatu) cewa ya yi: "Suna ta basarwa da ɓoye al'amura shi kuma Buhari ya warware komai. Ku zubar da takardun karatunku ku zama dakarun Nnamdi Kanu shashashai."
"Ku rabu da Buhari, ba shi da ƙwarewar mulki, ku tanadi ƙuri'aku ku sauya shi a 2023 domin samar da kyakkyawar Najeriya. Mu tabbata ba mu sake maimaita wannan kuskuren ba," a cewar wani mai suna D.U.C.E🗣 (@mazi_duce).
Sai kuma Daddy D.O (@DOlusegun) da ya ce: "Buhari ya kira yaƙin basasa abin baƙin ciki ƙarara...amma kuna tunanin Nnamdi kanu yana taimaka muku ne domin yaƙr Buharin ta hanyar sakin masu laifi daga gidan yari da kashe jami'an tsaro da ƙona asibitoci."
A shirye muke mu bayar da shawarar gyaran Najeriya - PDP
A nata martanin, babbar jam'iyyar adawa a ƙasar, Peoples Democratic Party (PDP) ta ce a shirye take tsaf domin bai wa mahukunta shawarar yadda za a kawo ƙarshen ƙalubalken da Najeriya ke fuskanta.
"A matsayinmu na jam'iyyar siyasa da ke da sha'awar ci gaba da kasantuwar kyakkyawar ƙasa, a shirye muke mu bayar da shawara da kuma taimakawa wajen fitar da Najeriya daga ƙalubalan da take fuskanta," a cewar wata sanarwa.
Sai dai ta ɗora alhakin halin rashin tsaron a kan gazawar shugaban wajen ɗaukar matakan da suka dace a yaƙi da 'yan bindiga.
'Buhari na fama tsohon raunin da ya warke'
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar YPP, Kingsley Moghalu ya bayyana kalaman na Buhari a matsayin "marasa daɗin ji" a matsayinsa na shugaban ƙasa, inda ya ce yana tuna wa mutane munanan abubuwan da suka faru a yaƙin Biafra.
"Tabbas yaƙi mummunan abu ne, dole ne mu guje shi. Amma idan kana cewa 'za mu bi da su da salon da suka fi ganewa' kana taso da wasu abubuwa ne marasa daɗi da aka aikata wa wata al'umma," in ji shi.
Shi ma Reno Omokri, tsohon mataimaki na musamman ga tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan, ya ce kalaman na Buhari "barazanar yaƙi ce yake yi wa 'yan kudu maso gabas".
Ƙarin labarai kan Biafra: