Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rikici tsakanin ƴan Nijar da ƴan Ivory Coast a Abidjan ya jikkata mutum 110
Gwamnatin Jamhuriyyar Nijar ta ce ta aika wani ayarin jami'ai zuwa ƙasar Ivory Coast bayan wani yamutsi da ya faru tsakanin 'yan ƙasar kuma ya ritsa da 'yan Nijar da dama.
Lamarin ya faru ne a ranar Laraba, bayan wani bidiyo da aka yaɗa inda ake nuna wasu jami'an tsaro na gallazawa wasu matasa da aka alaƙanta da cewa ƴan kasar Cote d'Ivoire ne, kuma aka ce lamarin ya gudana ne a Nijar.
Wannan lamari dai ya kawo rudani inda matasan wasu daga cikin unguwannin birnin suka kai farmaki ga 'yan kasar ta Nijar.
Bayanai dai na cewa tuni ƙura ta lafa, har ma ministan harkokin cikin gida na Ivory Coast ya ce an kama mutum 10 waɗanda ake zargi da hannu a rikicin na birnin Abidjan.
Ƴan ƙasar Nijar da dama sun samu raunuka sanadiyyar rikicin kuma an neman wasu da suka ɓace, baya ga asarar ɗumbin dukiya.
Haruna Seni mazaunin unguwar Ajame, ɗaya daga cikin unguwannin da lamarin ya shafa, ya shaida wa BBC cewa wadanda suka jikkata sun kai mutum 110 kamar yadda hukumomi suka sanar.
Ya ce: "Cikinsu akwai mutum biyu da suka galabaita, sai dai babu wanda ya mutu, sannan mutum uku sun ɓace ana nemansu.
"Sannan an yi asarar dukiya mai ɗumbin yawa an kuma lalata motoci da dama kusan guda biyar baya ga kudi. A yanzu komai ya lafa," a cewar Haruna Seni.
Ministan cikin gida na Ivory Coast ya ce a yanzu haka gwamnati ta dauki dukkan matakan da suka dace don gudanar da bincike da kuma gurfanar d duk wanda aka kamada hannu a rikcin.
"Tuni aka kama mutum 10 a wannan bincike da aka soma kuma za mu kama wanda ya yi bidiyon da duk wadanda suka yaɗa shi," in ji ministan.
Su ma hukumomin Jamhuriyyar Nijar sun bayar da tabbacin komai ya lafa, kamar yadda Ministan Harkokin Wajen Kasar ya fada, inda ya ce tuni shugaban ƙasa ya tura Ministan Harkokin Cikin Gida zuwa kasar Ivory Coast kan lamarin.
Ya ce: "Da farko Ministan Harkokin Cikin Gida na Ivory Coast ya ƙaryata bidiyon ya kuma nuna rashin jin daɗin ƙasar kan lamarin.
"A yanzu muna sa ido kan abin da ke faruwa a can Ivory Coast dangane da abin da ya shafi jama'armu," in ji shi.
A yanzu dai komai ya lafa kan rikicin wanfda ya faru a Abidjan babban birnin Ivory Coast, kuma wanda ya fi shafar al'ummar Hausawa ƴan Nijar mazauna can.