Rev Father Ejike Mbaka: Babban malamin Cocin ya bukaci 'yan majalisa su tsige Buhari

Asalin hoton, Nigeria presidency
Fitaccen malamin Cocin Katolikan nan da ke Najeriya, Rabaran Fada Ejike Mbaka, ya ce ya kamata shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sauka daga mulki idan ba haka ba a tsige shi.
Rabaran Fada Mbaka, wanda a baya a goyi bayan shugaban kasar, ya kara da cewa ya yi kiran ne saboda Shugaba Buhari ya gaza shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi Najeriya.
Malamin Cocin ya bayyana haka ne a gaban dimbin mabiyansa a Enugu da ke Kudu Maso Gabashin Najeriya.
"Idan da a kasashen da aka ci gaba ne da tuni Shugaba Buhari ya ajiye mukaminsa. Ku ambato ni a koina cewa na yi kira ga shugaba Buhari ya sauka daga mulki tun da girma da arziki.
Muna kuka ne saboda ba mu da jagora...idan ba za ka iya mulki ba, ka sauka ko a sauya ka...ko dai Buhari ya sauka da kansa ko kuma a tsige shi.."
Fada Mbaka ya kara da cewa duk da yake a baya ya goyi bayan Shugaba Buhari, ya yi hakan ne saboda a baya ya taka rawa "amma yanzu me ya sa ana kashe mutane amma babban jami'in tsarom kasa yana zaune bai ce uffan ba?"
A cewarsa 'yan bindiga suna kai hare-hare a kan kowanne bangare na kasar amma Shugaba Buhari ya gaza daukar matakin da ya dace domin shawo kan matsalar.
"Muna kira ga majalisar wakilai ta tsige shugaba Buhari. Idan kuma ta ki tsige shi ta koma fada da Fada Mbaka, to abin da ba su taba tunanin zai faru ba zai fada kan 'yan majalisar wakilai da na dattawa," in ji Malamin Cocin.
Malamin yana yin wanna kira ne a yayin da su ma masu amfani da shafukan sada zumunta a Najeriya musamman shafin Twitter sun fusata sakamakon matakin da hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta dauka na gayyatar Dr Usman Bugaje saboda ya soki gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
Dr Bugaje, wanda ya yi hira da gidan talbijin na AIT a makon nan, ya caccaki gwamnatin Buhari bisa gazawarta wajen tabbatar da tsaro a kasar musamman a Arewa.
Ya yi kira ga shugaban kasar da 'yan majalisun dokokin tarayya su sauka daga mukamansu idan ba za su iya tabbatar da tsaro a kasar ba.
"Idan ba za ku iya gyara matsalolin kasar nan ba, ya kamata ku sauka daga mulki. Me kuke yi a kan mukamanku? Su ma 'yan majalisar dokoki, suna zaune suna jin dadin albashi da sauran alawus-alawus yayin da kasar nan take rugujewa kuma babu abin da suke yi. Wannan kasar tana rugujewa amma kuna nan a zaune kuna ta bayar da uzuri," in ji Dr Bugaje.
'Gwamnatin Buharitana yi wa kanta babbar illa'
Wadannan kalamai sun jawo masa gayyata daga hukumar DSS inda wasu rahotanni suka ce ya kwashe tsawon wunin Laraba yana amsa tambayoyi inda daga bisani aka sake shi.
Masu lura da lamura da sharhi kan ci gaban Najeriya irin su Dr Mairo Mandara sun kwashe tsawon ranar suna jiran ganin an saki dan siyasar, wanda da shi aka kafa jam'iyyar APC mai mulkin kasar.
Ba wannan ne karon farko da fitaccen masanin yake sukar gwamnatin Shugaba Buhari ba saboda abin da ya kira gazawarta wajen tabbatar da tsaro a kasar.
Dr Bugaje, wanda dan asalin jihar Katsina ne da ke fama da hare-haren 'yan fashin daji da masu garkuwa da mutane, ya taba samun gayyata daga wurin Shugaba Buhari domin ya zama jakadan Najeriya a wata kasa amma ya ki karba yana mai cewa ci gaban arewacin Najeriya ne babban abin da zai sanya a gaba.
Me 'yan Twitter suke cewa?

Asalin hoton, OTHER
Gayyatar da DSS ta yi wa dan siyasar ta haifar da suka daga masu amfani da Twitter inda sunan Usman Bugaje ya kasance daya daga cikin manyan batutuwan da aka fi tattaunawa a shafin.
Da yake tsokaci kan batun, fitaccen mai sharhin nan kan harkokin yau da kullum, Farfesa Jibrin Ibrahim ya ce "gwamnatin [Buhari] tana yi wa kanta babbar illa saboda yadda take tsare da kuma musgunawa masu sukarta. Mun dade muna yaki domin tabbatar da 'yancin jama'a kuma babu wanda ya isa ya rufe mana baki."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Ita kuwa kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International jan hankali ta yi game da labarin gayyatar da DSS ta yi wa Usman Bugaje.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
A nata bangaren, 'yar Kafanchan, ta koka kan yadda mutane suke yin shiru yayin da Buhari yake "hukunta 'yan arewa da suka soki" gwamnatinsa tana mai cewa a bara ma sai da jami'an tsaro suka tsangwami matarsa saboda ta bayyana ra'ayinta kan matsalolin da kasar take ciki.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3
Karin labarai masu alaka:











