'Yan IPOB sun sake kai hari a wani ofishin 'yan sanda a Imo

Rahotanni daga jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya na cewa 'yan kungiyar IPOB da ke rajin ballewa daga Najeriya sun sake kai hari a wani ofishin 'yan sanda.

Rundunar 'yan sandan jihar ta Imo ta ce an kai harin ne a ofishinta da ke karamar hukumar Ehime Mbano ranar Talata da yamma.

Mai magana da yawun rundunar Orlando Ikeokwu, ya shaida wa BBC cewa maharan sun kona ababen hawa uku kodayake ba su kashe 'yan sanda ba.

Lamarin na faruwa ne a yayin da mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya kai ziyara a birnin Owerri na jihar ta Imo domin duba barnar da 'yan kungiyar suka yi yayin harin da suka kai kan hedikwatar 'yan sanda da gidan yari ranar Litinin.

Kazalika wannan hari na zuwa ne a yayin da shugaban Najeriya ya nada Usman Alkali Baba a matsayin sabon Mukaddashin Babban Sufeton rundunar 'yan sandan kasar domin maye gurbin Mohammed Adamu.

Rundunar 'yan sandan ta aike da karin dakarunta na kwantar da tarzoma zuwa jihar Imo, bayan ta zargi kungiyar IPOB da hannu wajen kai hari kan hedikwatarta da kuma gidan yarin jihar.

"Binciken da aka fara gudanarwa ya gano cewa maharan da suka kai harin suna da yawa kuma dauke da muggan makamai irin su AK-47 sannan kuma mambobi ne na kungiyar IPOB," a cewar sanarwar da kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya Frank Mba ya fitar.

'Fursunoni 1,844 sun tsere'

A nata bangaren, hukumar kula da gyaran hali ta Najeriya ta ce 'yan bindiga sun kubutar da fursunoni 1,844 daga gidan yarin birnin Owerri na jihar Imo.

Hukumar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da mai magana da yawunta Francis Enobore ya fitar ranar Litinin.

'Yan bindigar sun yi amfani da manyan bindigogi masu sarrafa kansu da nakiyoyi wajen fasa gidan yarin, a cewar hukumar.

"A kididdiga ta karshe, fursunoni 6 sun dawo don radin kansu cikin gidan yarin yayin da fur 35 suka ki amincewa su tsere a yayin harin", in ji sanarwar.