Mohamed Bazoum: Sabon shugaban Jamhuriyar Nijar ya sha rantsuwar kama aiki

Zababben shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum, ya sha rantsuwar kama aiki bayan ya lashe zaben da Kotun Tsarin Mulkin kasar ta tabbatar da nasararsa.
Shugaban Kotun Kolin mai shari'a Bouba Mahaman ne ya rantsar da Mohamed Bazoum a gaban mambobin Kotun Tsarin Mulki.
Sabon shugaban kasar ya rantse da Al-Kur'ani mai tsarki yana mai shan alwashin gudanar da mulki bisa doka da oda.
Shugabannin kasashe da na gwamnati da dama ne suka halarci bikin wanda aka yi Yamai, babban birnin kasar bisa tsauraran matakan tsaro.
An rantsar da sabon shugaban ne kwana biyu bayan wani yunkurin juyin mulki da ya ci tura a kasar. Hukumomi sun ce sun dakile yunkurin na ranar Laraba.
Shugaba mai barin gado Issoufou Mahamadou ya mika wa sabon shugaban kasar tutar Jamhuriyar Nijar da ke nuna sauya mulki daga hannusa zuwa hannun Mohamed Bazoum.
Wannan ne karon farko a tarihin dimokradiyyar Jamhuriyar Nijar da gwamnatin farar hula take mika mulku ga wani zababben shugaban farar hula.
A watan da ya gabata ne Kotun Tsarin Mulkin kasar ta Jamhuriyar Nijar ta tabbatar da Mohamed Bazoum a matsayin wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasar Nijar da aka yi zagaye na biyu.
Mohamed Bazoum na jam'iyya mai mulki ta PNDS Tarayya ya ci zaben da kashi 55.66 cikin 100 na kuri'un da aka jefa abin da ke nufin ya zarce tsohon shugaban kasar kuma dan takarar jam'iyyar Tchanji Alhaji Mahamane Ousmane, wanda ya samu kashi 44.34.
Sai dai Mahamane Ousmane ya ce zai kalubalanci sakamakon zaben.
Kalubalen da ke gabansabon shugaban

Asalin hoton, Getty Images
Sharhi daga Ishaq Khalid, BBC Hausa, Abuja
Jamhuriyar Nijar, mai yawan al'uma kimanin muliyan 23, tana daga cikin kasashe mafiya talauci a duniya a cewar alkaluman Majalisar Dinkin Duniya.
To amma a 'yan shekarun nan ta gano dimbin arzikin man fetur lamarin da ya kara sanya fata a zukatan talakawan kasar cewa za a yi amfani da arzikin yadda yakamata domin kyautata yanayin rayuwarsu.
Kasar tana kuma da dimbin arzikin makamashin yuraniyom da albarkatun noma. Wani rahoton baya-bayan nan na Bankin Duniya ya ce Nijar ta dan samu ci gaba wajen yaki da talauci, ko da ya ke dai har yanzu akwai jan aiki wajen raba jama'ar kasar da matsalar ta talauci.
'Yan kasar da dama musamman matasa na fatan samun saukin matsalar rashin aikin yi.
Haka nan sabon shugaban kasar zai tarar da manyan kalubale ta fuskar tsaro - ciki har da tayar da kayar baya na Boko Haram a kudancin kasar kusa da iyakarta da Najeriya, da kuma hare-haren kungiyoyin tayar da kayar baya masu alaka da al-Qa'ida da IS a yammacin kasar kusa da iyaka da kasashen Burkina Faso da Mali.
Daga watan Janairu zuwa watan Maris na wannan shekarar kadai, masu tayar da kayar baya sun kashe mutane fiye da 300 a hare-hare kan kauyuka a jihohin Tillaberi da Tahoua yayin da suke ci gaba da yin barazana ga sha'anin tsaro. Akwai dimbin 'yan gudun hijira a kasar sanadiyyar matsalar tabarbarewar tsaron.
Cikin jawabinsa yayin bikin rantsuwar, sabon shugaban kasar, Mohamed Bazoum, ya yi alkawarin jajircewa wajen magance matsalar ta tsaro. Ya kuma ce zai yi kokarin shimfida adalci a mulkinsa.
Sabon shugaban na Nijar zai kuma fuskanci dimbin kalubale ta fuskar siyasa. Ko da ya ke Nijar ta yi nasarar sauya gwamnati salin alin daga zababben shugaban kasa zuwa wani zababben shugaban bisa tsarin dimokuradiyya a karon farko tun bayan samun mulkin kanta daga Turawan Faransa a 1960, to amma zaben shugaba Mohamed Bazoum ya bar baya da kura.
An samu rarrabuwar kawuna a kasar ta fuskar siyasa inda har yanzu 'yan adawa ke cewa ba su yarda da zabensa ba, suna zargin an tafka magudi.
Haka nan kwana biyu kacal kafin rantsar da sabon shugaban na Nijar, wasu sojoji sun yi yunkurin juyin mulki wanda bai yi nasara ba - inda aka yi ta harbe-harbe a kusa da fadar shugaban kasar dake birnin Niamey.
Hukumomi sun bayyana cewa sun kama wasu daga cikin wadanda ake zargi da hannu a yunkuri.
Don haka wani babban kalubale dake gaban sabuwar gwamnatin karkashin jagorancin Mohamed Bazoum, shi ne na tabbatar da hadin kan kasa a siyasance, da kuma samun biyayyar illahirin rundunonin tsaron kasar domin ya tafiyar da mulkinsa babu babbar tangarda.











