'Yan bindiga sun sace ɗalibai 30 daga kwalejin gandun daji da ke Kaduna

School Kidnapping

Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da sace ɗalibai 30 daga Kwalejin Horar da Harkokin Noma da Abubuwan da suka shafi Gandun Daji ta gwamnatin tarayyya wato Federal College of Forestry Mechanisation a unguwar Mando a cikin garin Kaduna.

Kwamishinan harkokin tsaro na jihar, Samuel Aruwan a cikin wata sanarwa ya ce kawo yanzu ba'a san inda dalibai 30 suke ba amma Sojojin Najeriya sun ceto mutane 180 da akasari daliban kwalejin.

"Sojojin Najeriyar sun samu nasarar ceto mutanen 180; dalibai mata 42, da malamai takwas da kuma dalibai maza 130. Amma kuma har yanzu ba a gano sauran dalibai maza da mata kusan 30 ba", in ji Aruwan.

'Yan bindigar su da yawa sun kai hari a makarantar ne da misalin karfe sha daya da rabi na daren Alhamis, inda suka sace dalibai da dama har da malamai.

Kawo yanzu kusan ɗalibai 800 aka sace tun watan Disamba kuma wannan ne karo na uku da aka sace ɗalibai daga makarantunsu a shekarar 2021 a Najeriya.

Sanarwar ta kara da cewa "dakarun sojin suka kai dauki cikin makarantar inda suka fafata da 'yan bindigar. Wasu daga cikin daliban da aka ceto sun samu raunuka, kuma suna ana duba lafiyarsu a wani asibitiin sojoji na Kaduna."

Wasu daga cikin daliban da aka ceto

Asalin hoton, Kaduna State Govt

Bayanan hoto, Wasu daga cikin daliban da aka ceto

Aruwan ya kara da cewa "yanzu haka gamayyar dakarun sojojin kasa da na sama da jami'an tsaron farin kaya na cigaba da aikin bin diddigin sauran daliban da 'yan bindigar suka yi awon gaba da su."

Wata ɗalibar makarantar ta shaida wa BBC cewa cikin dare maharan suka shiga makarantar.

Ta ce kusan rabin ɗalibai mata aka tafi da su a makarantar kuma ba a tafi da ɗalibi namiji ko ɗaya ba.

Jami'an tsaro a gaban makarantar

Wani mazunin unguwar Mando a jihar ta Kaduna ya bayyana cewa kusan karfe 11 da rabi na dare zuwa 12 sun rika jin harbi amma sun yi zaton a Makaratar Horar da Sojoji ta NDA ne ake yi.

"Dama wani lokaci a NDA su kan yi harbi cikin dare tunda makarantar sojoji ce, don haka mun yin tunanin abin da ke faruwa kenan. Sai da ssuba da muka fita sallah en muka samu labarin abin da ya faru," a cewarsa.

Mutumin ya bayyana cewa kawo yanzu jami'an tsaro na kewaye da makarantar kuma an kwashe ragowar daliban da ba a sace ba an tafi da su makarantar NDA.

Kwalejin na makwabtaka da makarantar NDA duk a nan Mando.

Wakilin BBC Yusuf Tijjani da ya je makarantar ya tabbatar da ganin jami'an tsaro a makarantar da iyaye da suka yi dafifi a bakin kofar makarnatar.

Ya ce ana kidayar ɗaliban da suka rage kawo yanzu waɗanda ba a yi awon gaba da su ba.

Ya kuma ce wasu jami'an tsaro sun ga ƙunson harsasai a cikin makarntar kuma suna aikin tantance su.

Ya bayyana mana cewa akwai ɗalibai kusan 300 a makarantar amma har yanzu babu tabbas kan yawan ɗaliban da aka sace.

Yusuf Tijjani ya bayyana cewa cikin kokarin da jami'an tsaro ke yi har da jiragen sojoji suna shawagi a sama.

Unguwar Mando dai tana bisa titin da ke zuwa tashar jirgin kasa da filin jirgin saman jihar Kaduna don haka ba ta rabo da jama'a. Haka kuma, tana hanyar garin Birnin Gwari ne mai fama da matsalar rashin tsaro tun da dadewa.

KIdnapping