Mahamane Ousmane: Abin da ya sa zan kalubalanci sakamakon zaben Jamhuriyar Nijar

Dan takarar shugaban kasa da ya sha kaye a zaben da aka gudanar a Jamhuriyar Nijar ranar Lahadi, Alhaji Mahamane Ousmane, ya ce zai kalubalanci sakamakon zaben.

Alhaji Ousmane, wanda ya yi takara a karkashin jam'iyyar RDR -CANJI, ya yi zargin cewa an tafka magudi a zaben na zagaye na biyu wanda dan takarar jam'iyya mai mulki ta PNDS Tarayya Mohamed Bazoum ya yi nasara.

Alkaluman da hukumar zabe mai zaman kanta ta CENI ta fitar sun nuna cewa Bazoum ya samu sama da kuri'a miliyan 2 da dubu 501.

Shi kuma Mahamane Ousmane ya samu kuri'a sama da miliyan 1 da dubu 968.

Bazoum ya samu kashi 55.75 na kuri'un da aka kada, yayin da Mahamane Ousmane, wanda tsohon shugaban kasar ne, ya samu kashi on 44.25.

Sai dai yayin da yake jawabi daga Damagaram, Alhaji Mahamane Ousmane, ya yi zargin cewa shi ne ya yi nasara a zaben da kuri'a fiye da kashi 50 cikin dari yana mai cewa an murde masa zaben.

A cewarsa: "A lokacin zaben, mun gano magudi mai dimbin yawa mussaman a yankin Tahou, Agadez da Arewacin Maradi da Arewacin Zinder. Wannan coge ya watsu a ko ina cikin fadin kasar Nijar.

Magudi mafi muni wanda ya fito karara shi ne a Agadez yankin Timiya inda masu kada kuri'a da suka fito suka zarta wadanda suka yi zabe yawa da kashi 103 bisa dari, kuma dan takarar jam'iya mai mulki ya samu kasha 99 cikin 100 na kuri'un da aka kada.,' in ji shi.

Ya kara da cewa "a wadannan yankuna da bindigogi aka sa wakilanmu saka hannu kan takardun sakamako ba tare da sun rubuta abin da ya wakana ba."

"A yankin Tahou, wurare 15 ne aka samu irin wannan manya-manyan rashin biyar ka'idar zabe. A rumfunan zabe na Dabaga da Tagriss tun jajiberin zabe ne aka kammala zabe. An samu takardun kada kuri'a na bogi wadanda hukumar zabe ta CENI da kanta ta sanar a cikin wata sanarwa da ta yi a ranar 21 ga watan Febuwari 2021. Kuma game da hakan babu wani mataki da aka dauka domin bambata kuri'a ta kwarai da ta boge. Wadanda suka yi wannan kazamin aiki ba a ce masu komai ba game da doka," a cewar Mahamane Ousmane

Dan takarar na jam'iyyar RDR -CANJI ya kara da cewa a jihar Damagram a garin Belbaji an kirga kuri'u na mazabu 45 da "ba su ko buda ba a ranar zabe. A garin Tenahi da Tasker, an kwace akwatunan zabe ne da bindigogi."

Tsohon shugaban kasar ta Jamhuriyar Nijar ya ce: "Amma duk da hakan sakamakon da ke gare mu daga wakilanmu ya tabbatar da nasarar mu da kashi 50 da digo 30 cikin dari na kuri'u a yayin da dan takara na bangaren masu iko ke da kasha 49,70. Saboda haka mun yi fatali baki daya da sakamakon zabe da aka bayar a wuraren da ba a bi ka'idodin zabe ba."

Ya ce za su bi dukkan hanyoyin da suka dace domin kare nasarar da ya yi ikirarin samu.

A baya dai wasu shugabannin jam'iyyun da suka mara wa jam'iyyar PNDS Tarayya baya wajen yin nasara a zaben sun shaida wa BBC cewa ikirarin da 'yan hamayyar suka yi na lashe zabe ba gasiya ba ne, suna masu cewa sun tayar da rigima ne kawai "saboda sun riga sun shirya cea idan ba su ne suka yi nasara ba, to ba za su amince da sakamakon zaben ba."

Kawo yanzu dai, hukumar CENI ba ta ce komai a kan wadannan zarge-zarge ba, kodayake kotun nan gaba ne ake sa ran kotun tsarin mulki za ta tabbatar da sakamakon zaben.