Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mohamed Bazoum: Wane ne sabon zaɓaɓɓen shugaban Nijar?
Mohamed Bazoum ya daɗe yana gwagarmayar siyasa a Jamhuriyyar Nijar wanda ya assasa jam'iyyasa ta PNDS Tarayya.
Bazoum balarabe ne ɗan jihar Damagaram wanda aka haifa a 1960.
Ya yi karatunsa na firamare har zuwa sakandare a Zinder kafin ya tafi jami'a inda ya karanci ilimin falsafa 1984.
Bazoum malamin makaranta ne inda ya koyar da ilimin falsafa a 1985 zuwa 1989 a Tahoua daga nan kuma ya koma Maradi ya ci gaba da koyarwa a fannin falsafa da ya ƙware.
Bazoum ya fara gwagwarmaya ne a ƙungiyar malaman makaranta kan neman hakkin ma'aikata da hakkin siyasa.
Wannan gwagwarmayar ce ta kai ga kafa jam'iyyar PNDS Tarayya bayan Bazoum ya haɗu da Mahamadou Issouou ta hanyar gamayyar ƙungiyoyin kwadago a wani taron kasa.
Bazoum yana cikin waɗanda suka tabbatar da zaben Mahamadou Issoufou.
Daga gwagwarmaya zuwa siyasa
Bazoum ya shaida wa BBC cewa tun farkon rayuwarsa yana da ra'ayin siyasa kuma a cewarsa ya yi karatun falsafa ne don ya yi tasiri ga burinsa na siyasa.
Ya ce gwagwarmayar ta shafi neman haƙƙin siyasa kuma ya shiga siyasa ne ta amfani da ƙungiyoyin ƙwadago.
"Mun yi amfani da ƙungiyoin ƙwadago don cimma burin jam'iyyun siyasa."
Muƙaman da Bazoum ya riƙe
Bazoum shi ne shugaban jam'iyyar PNDS Tarayya tun 2011.
Bazoum ya yi wa Mahamadou Issoufou mataimakin shugaban jam'iyyar PNDS Tarayyar kafin Issoufou ya zama shugaban ƙasa a 2011.
Ya rike muƙamin sakataren harakokin waje ƙarƙashin ma'aikatar harakokin ƙasashen waje a zamanin gwamnatin riƙon ƙwarya ta Amadou Cheiffou daga 1991 zuwa 1993.
An zaɓe shi ɗan majalisa ƙarƙashin jam'iyyar PNDS a zaɓen da aka gudanar a 1993 kafin soke zaɓen.
An fara naɗa Bazoum ministan harakokin ƙasashen waje a 1995 zamanin gwamnatin hadin guiwa tsakanin MNSD Nasara da PNDS Tarayya ta Hama Amadou yana matsayin Firaminista.
Gwamnatin Ba'are Mainasara ta sake naɗa shi muƙamin bayan juyin mulki a 1996, kafin ta tuɓe kan adawa da gwamnatin Mainasara.
Ya riƙe muƙamin ministan harakokin waje sau biyu daga 1995 zuwa 1996 da kuma 2011 zuwa 2015.
An sake zaɓen Bazoum a matsayin ɗan majalisa a 2016, kuma bayan sake rantsar da Issoufou a wa'adi na biyu ya naɗa Bazoum ministan harakokin cikin gida.
Ya kuma riƙe muƙamin minista a fadar shugaban ƙasa a 2015 kafin ya zama ministan harakokin cikin gida a 2016.
Bazoum ya yi murabus domin takarar shugaban ƙasa.