Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mutum bakwai sun mutu a hatsarin jirgin sama a Abuja
Mutum bakwai ne suka mutu a hatsarin jirgin saman soji ranar Lahadi a Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja.
Kakakin rundunar sojin sama ta Najeriya Air Vice Marshal Ibikunle Daramola ya ce dukkanin mutum bakwai da ke cikin jirgin ne suka mutu a hatsarin.
Ya ƙara da cewa babban hafsan sojin sama ya bayar da umurnin kaddamar da bincike kan musabbabin hatsarin.
Ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika ya ce jirgin mai suna King Air 350 ya yi hatsari ne bayan ya samu matsalar na'ura a lokacin da ya tashi sama, kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter.
Vice Marshal Daramola ya faɗa wa BBC cewa jirgin na kan hanyarsa ta zuwa ceton mutum 42 ne da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a Jihar Neja kafin ya juya zuwa Abuja saboda matsalar na'ura.
Jirgin wanda ba shi da girma ya faɗo ƙasa a kusa da garin Basa da ke babban birnin ƙasar, Abuja.
Waɗanda suka gane wa idonsu sun faɗa wa BBC cewa sun ji ƙara mai ƙarfi kafin jirgin ya kama da wuta.
Tazarar kilomita 100 ne tsakanin Minna, babban birnin Jihar Neja, da kuma Abuja.
Bayanai sun ce jirgin yana cikin wadanda Najeriya ta yi sayo domin ayyukan tsaro da leken asiri a ƙasar.