Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Joe Biden : Zai taimakawa ƙasashe matalauta da rigakafin korona
Fadar White House ta ce Shugaba Biden zai yi alƙawarin dala biliyan huɗu don shirin rigakafin cutar korona na kasa da kasa da zummar taimakawa ƙasashe matalauta.
Zai bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa da shugabannin manyan kasashen duniya masu karfin tattalin arziki a ranar Juma'a da za a yi ta bidiyon kai tsaye.
Jami'an Amurka sun ce za a saki dala biliyan biyu a karshen wannan watan, tare da sauran da za a biya cikin shekaru biyu masu zuwa.
Gwamnatin Amurka da ta gabata, a ƙarkashin tsohon shugaban ƙasar Donald Trump, ta ƙi shiga shirin allurar rigakafin na duniya, wanda aka fi sani da COVAX a taƙaice.
Hukumar Lafiya ta Duniya ce ke jagorantar shirin, wanda Shugaba Biden ya koma cikinta bayan rantsar da shi a matsayin shugaban Amurka a ranar 20 ga watan Janairun 2021.
Shi dai tshon shugaban ƙasar Donald Trump ya fice daga hukumar tun kafin ya sauka daga kan mulki, saboda zargin da yake yi mata na fifita China a kan Amurka ta fuskar yaƙi da korona.
Amurka ce a kan gaba wajen yawan waɗanda suka kamu da cutar korona a duniya, ko da yake a yanzu adadin na ci gaba da yin ƙasa, sakamakon sake inganta shirin yi wa yan ƙasar rigakafin cutar da sabuwar gwamnati ta bijiro da shoi.
Mista Biden ya yi alkawarin yi wa Amurkawa Miliyan 100 rigakafin cutar a kwanaki 100 na farkon mulkinsa, amma a yanzu ya ce za su zarce adadin da suka sanya nesa ba kusa ba.