Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda ɗaliba ta je makaranta da bindiga don harbe malamin da ya ce ta aske gashinta a Cross River
Wata yarinya ta je makaranta a jihar Cross River da bindiga ƙirar gida don harbe wani malaminta da ya umarce ta da aske gashinta.
Wani da ya shaida lamarin Otunva Charles Edem, ya shaida wa sashen BBC Pidgin cewa hakan ya faru ne a wata makarantar sakandare ta gwamnati da Ikot a yankin Akpabuyo ja jihar Cross River da ke kudancin Najeriya.
"Lamarin ya faru ne ranar Alhamis ɗin da ta gabata, a lokacin da yarinyar ta koma makaranta sai malaminta ya ce ta je aske gashinta da ta rina. Saboda a trsarin makarantu a jihar ɗalibai ba sa barin gashinsu ya taru balle har su rina shi, don haka dole ta koma.
"Washe gari sai ga shi ta tafi makarantar da bindiga. Shugabar makarantar ce ta fara lura da abin da ke faruwa. Sai mutanen da ke wajen suka taru suka riƙe ta, malamai da ɗalibai kuma suka fito baki ɗayansu."
Edem ya ce a lokaicn ya je wajen wani abokinsa ne da yake zaune a kusa da makarantar, sai suka ji hayaniya suka yi saurin shiga don ganin me yake faruwa a makarantar.
Daga nan ne kuma ya ɗauki hoton yarinyar d abindigar a hannunta.
Edem ya ce sun yi ƙoƙarin gano yadda aka yi ta samu bindigar sai ta kai su wajen wani tsoho.
"Daga nan ne muka gao cewa shi wannan tsohon mutumin ya kan yi lalata da ita ne kuma a wajensa ta samu bindigar."
Edem ya ce tuni suka miƙa ta ga hukumomi don yin binciken da ya dace.
Ya ce sai a jiya Laraba ne ya wallafa hoton yarinyar inda ya fara yaɗuwa a shafukan sada zumunta, inda mutane ke mamakin yadda yarinya za ta ɗauki bindiga ta je makaranta da ita don harbin malaminta.
A lokacin da sashen BBC Pidgin ya tuntuɓi mai magana da yawun rundunar ƴan sanda jihar Cross Irene Ugbo, sai ta ce "tun da kun ji labarin sai ku je ku wallafa idan kuna so, dole e sai na tabbatar muku, ina kwance a gadon asibiti ku kuma kuna damuna."