Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kano: Ana ce-ce-ku-ce kan bai wa ƴan kasuwa yankin da ke kusa da Gwauron Dutse
Ce-ce-ku-ce ya ɓarke tsakanin gwamnatin Kano da masana tarihi kan matakin da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta dauka na bai wa 'yan kasuwa wani yanki da ke gefen Gwauron Dutse.
Lamarin ya faru ne sakamakon ganin manyan motocin rusa gine-gine suna rushe katangar da aka kewaye Dutsen ana kuma kafa katakwaye domin yin rumfuna.
Gwauron Dutse tare da Dala da ke tsakiyar birnin Kano na cikin abubuwan tarihi da Kanawa suke alfahari da su lamarin da ya sa ake tayar da jijiyoyin wuya game da matakin da gwamnatin jihar ta dauka na yanka gefensa domin bai wa 'yan kasuwa.
Sai dai Gwamnatin jihar ta Kano ta ce ta bai wa 'yan kasuwar Katako da ke Sabon Gari wani yanki na gefen Gwauron Dutse ne domin su ji dadin yin kasuwanci.
Architect Sulaiman Abdulwahab, shugaban hukumar tsara birane ta Kano, KNUPDA, ya shaida wa BBC cewa sun bayar da filin aro ne ba sayarwa suka yi ba.
"Akwai mutane a cikin kasuwar Sabon Gari wadanda suke zaune a wuraren da ba nasu ba, sai gwamnati ta ce maimakon a tashe su haka kawai tun da su ma 'yan jiha ne me zai hana a samar musu wani wuri. Sai ake gyarawa za a ajiye su wadannan masu sana'ar kujera, kuma ba a kan tsaunin aka ajiye su ba, a gefe.
"Ba sayarwa za a yi ba, ba su za a yi. Kuma bai hana gwamnati ta danƙa musu shi ya zama dindindin ko kuma bai wuce su dan bayar da abin haraji ba.
Sai dai masana tarihi sun soki daukar wannan mataki wanda suke ganin yunƙuri ne na kawar da tarihin Kano.
Fitaccen malamin tarihin nan da ke Kano, Dr Tijjani Naniya, ya shaida wa BBC cewa gwamnatin Kano na son zubar da mutunci da tarihin jihar.
"Gwauron Dutse yana cikin duwatsun da jama'a suke zaune a wajen, da na Dala da kuma na Tinagar da na Jigirya da na Magwan. Sun shafi martabar Kanawa da mutuncinsu da al'adarsu da kuma tarihinsu.
A cewarsa tun zamanin tsohon Gwamna Rabi'u Kwankwaso aka so yin wani abu a wurin amma marigayi Sarkin Kano Ado Bayero ya bai wa tsohon gwamnan shawarar kada ya taba Gwauron Dutse kuma ya bari.
Ya kara da cewa a lokacin tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau an kewaye wurin domin gudun kada wasu su taba shi.
Wasu mazauna jihar ta Kano sun goyi bayan gwamnati yayin da wasu ke adawa da shi.
Ba wannan ne karon farko da gwamnatin jihar take shan caccaka cefanar da wasu yankuna na jihar ga 'yan kasuwa.
Sai dai gwamnati ta sha cewa ana cefanar da wuraren ne domin samun kudaden shiga da kuma tabbatar da tsaro.