'Tambayar yaushe za ki yi aure tana ƙona min rai'

Kusan kowa ya san yadda ake matsa wa mutane su yi aure a yankinsu. Tambayar "yaushe za ki yi aure" na cikin abubuwan da suka fi ɓata wa 'yan mata rai a rayuwarsu.

"Mutanen da suke matsa wa mutum sun haɗa da danginsa da abokan aiki da waɗanda kuke zuwa wurin ibada tare, wani zubin ma har sai sun ɓata maka rai," a cewar wata lauya mai shekara 27 mai suna Ebunoluwa Tengbe.

A cikin shirin Sashen Ingilishi na BBC mai suna The Comb, wasu mata matasa biyu sun bayyana abin da ke ci musu tuwo a ƙwarya game da tambayar "wai yaushe za ki aure ne".

Abokan aikinta a ofis da ke Freetown kan uzura mata cewa tana shafe lokaci mai yawa a wurin aiki, kamata ya yi ta riƙa samun lokacin kula maza a madadin haka.

"Ba na cikin wata damuwa - ba na jin wata raguwa a jikina har sai lokacin da irin waɗannan tambayoyin suka fara yin yawa, sai kuma ki ji kin fara tantamar halayenki," in ji matashiyar 'yar ƙasar Saliyo.

Haka ma abin yake a Tanzania, in ji 'yar jarida mai suna Tulanana Bohela.

Bayan wani taron horarwa, wani mutum ya yi tambayar cewa wai me ya sa Bohela ba ta yi aure ba sannan ya buƙace ta da zama "mai sauƙin kai" da "tawali'u" ko ta samu miji.

Kazalika, akwai wata ƙanwar mahaifiyarta da ke yi mata addu'a a gaban mutane don ta samu miji a wurin taron danginsu.

"Ina cikin mata 'yan ƙalilan da har yanzu ban bar gaban iyayena ba zuwa gidan miji," a cewarta.

Sai dai 'yar shekara 33 ɗin tana zaune ne ita kaɗai, abin da ta ce yana janyo ce-ce-ku-ce a ƙasarsu. Wani lokacin takan faɗa wa mutane cewa tana zaune ne tare da ɗan uwanta don a sauƙaƙa mata.

Ita ma kanta wadda ta gabatar da shirin na wannan makon, Damilola Odulowu, na fuskantar matsin "wai yaushe za ki aure" a Najeriya.