Ƙasashe 20 da Saudiyya ta haramta wa shiga ƙasarta

Haramcin shiga Saudiyya daga ƙasashe 20 ya fara aiki, a wani mataki da ƙasar ta ɗauka don daƙile yaɗuwar korona.

A ranar Laraba ne gwamnatin Saudiyya ta sanar da haramta wa baƙi daga ƙasashe 20 shiga ƙasarta. Kuma haramcin ya shafi jami'an diflomasiyya da na lafiya, kamar yadda kamfanin dillacin labaran ƙasar na SPA ya ruwaito.

Haramcin ya fara aiki tun da misalin ƙarfe 9 na dare agogon ƙasar. Kuma haramcin ya shafi duk wanda ya yi makwanni biyu a ɗaya daga cikin ƙasashen 20 kafin ya shigowarsa Saudiyya ko kuma ya yada zango a ɗaya daga cikin ƙasashen.

Ƙasashe 20 da haramcin ya shafa:

  • Argentina
  • Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa
  • Jamus
  • Amurka
  • Indonesia
  • Ireland
  • Italiya
  • Brazil
  • Portugal
  • Birtaniya
  • Turkiya
  • Afirka Ta Kudu
  • Sweden
  • Switzerland
  • Faransa
  • Lebanon
  • Masar
  • Indiya
  • Japan
  • Pakistan

Saudiyya ba ta bayyana ranar ɗage haramcin ba, duk da ta ce matakin na wuccin gadi ne.

Haramcin zai iya shafar ƙasashe kamar Najeriya da mafi yawanci ƴan ƙasar ke yada zango wasu daga cikin ƙasashen da haramcin ya shafa kamar Masar da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa kafin isa Saudiyya.

Matakin na zuwa ne bayan ministan lafiyar Saudiyya Tawfiq al-Rabiah ya yi gargaɗin cewa za a ɗauki sabon matakin kullen korona idan har ƴan ƙasar da mazauna ba su kiyaye matakan da aka ɗauka ba.

Zuwa ranar Laraba mutum 368,000 cutar korona ta shafa a Saudiyya, inda ta kashe mutum kusan 6,400, wanda shi ne adadi mafi yawa a yankin ƙasashen tekun fasha.

Yawan masu kamuwa da cutar a rana sai ƙaruwa yake kusan a kullum tun daga watan Yunin bara.

A watan Disamba Saudiyya ta ƙaddamar da aikin yin rigakafin korona a ƙasar bayan ta karɓi kason farko na allurar ta Pfizer-BioNTech