Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Amurka : Biden zai sake haɗa jariran da gwamnatin Trump ta ƙwace daga hannun iyayensu
Shugaba Joe Biden ya ɗauki matakan farko don sauya wasu daga cikin tsaauraran dokokin gwamnatin Trump da ke adawa da bakin haure.
Ya sanar da ƙirƙirar wani kwamiti don sake haɗa jariran da gwamnatin Trump ta raba su da iyayensu a kan iyakar Amurka da Mexico.
Da yake sanya hannu kan umarnin a Fadar White House, Mista Biden ya ce za su warware ''Rashin imani gwamnatin da ta shude''
A ranar Talata, majalisar dattijan Amurka ta tabbatar da wani lauya ɗan asalin Cuba, Alejandro Mayorkas, a matsayin Sakataren hukumar tsaron Cikin gida ta Homeland.
Ya zama bakon haure na farko da ya jagoranci hukumar da ke kula da batutuwan shige da fice da kan iyaka.
Kuri'ar da aka kaɗa don tabbatar da shi ta nuna irin farraƙun dake akwai tsakanin sanatocin Republican da Democrat, don yawancin ƴan Republican basu yarda da shi ba.
An tsare dubban iyaye da yara da ke shiga kasar ta kan iyaka, waɗanda da yawansu ke tserewa rikici a ƙasashen Honduras da El Salvador da kuma Mexico.
A yayin yaƙin neman zaɓensa a 2016, shugaba Donald Trump ya mayar da hankali sosai a kan alƙawuran harkokin tsaro a iyakar Amurka.
Ya cika alƙawarin da ya yi na gina katanga a kan iyakar kasar da kudancin Mexico, ko da yake bata kai irin wadda ya yi alƙawari ba, sannan ba Mexico ce ta biya kuɗin aikin ba kamar yadda ya alƙawarta.