An tono wasu gawawwaki masu shekaru 2,000 da aka adana da harshen zinari a Masar

Gawawwakin da aka adana harshen zinari a Masar

Asalin hoton, Egyptian Ministry of Antiquities

Bayanan hoto, Ana tunanin an binne matattu da zinari mai kama da harshe shekaru fiye da 2,000 don su iya magana a lahira.
Presentational white space

Masu binciken kayan tarihi sun tono gawawwaki da aka binne da harshen zinare fiye da shekara 2,000 a cikin bakinsu a arewacin Masar, kamar yadda ma'aikatar adana kayan tarihi ta ƙasar ta bayyana

Wata tawagar kiristocin Masar ƴan Dominican da ke aiki wurin ibadar Taposiris Magna a Alexandriane ce ta gano ƙaburbura 16 da aka binne gawarwakin a zamanin Girkawa da Romawa.

A ciki gawawwaki ne da aka adana.

Ana tunanin an rataya wa matattun layu ne da kuma zinari masu kama da harshe don su yi magana a gaban ubangiji a ranar lahira.

Mutanen Misrawa a can baya sun yi imani da wani Osiris a matsayin ubangijin lahira da kuma alƙalin matatattu.

An sassaƙa wanda suke yi wa bauta da katako da yi masa kayan ado na zinari - wanda yake ɗauke da ɗaya daga cikin gawawwakin, kamar yadda ma'aikatar adana kayan tarihi ta ambato jagoran nazarin kimiyyar kayan tarihi Kathleen Martinez na Jami'ar Santo Domingo tana cewa.

An ga kamar kambi a yadda aka ƙawata ɗaya daga cikin gawawwakin da ƙaho da kuma maciji, a cewarta. A kirji kayan adon ya nuna abin wuya da aka rataye - wata alama ta abin bautarsu Horus

Gawawwakin da aka adana harshen zinari a Masar

Asalin hoton, Egyptian Ministry of Antiquities

Bayanan hoto, An fuskar mace da aka binne da wasu kayan zinari
Presentational white space

Khaled Abo El Hamd, babban daraktan hukumar kula da kayan tarihi a Alexandria ya ce aikin binciken kayan tarihin a Taposiris Magna ya kuma gano fuskar mace da aka binne da wasu kayan zinari da wasu abubuwa da suka samo asali tun zamanin Girkawa da Romawa.

Ma'aikatar adana kayan tarihi ta ce an gano sululalla da dama da ke ɗauke da sunan hoton sarauniya Cleopatra ta bakwai.

Cleopatra VII ita ce sarauniyar Girkawa daga Ptolemaic ta ƙarshe, wacce ta yi mulki a Masar daga 51 zuwa 30 kafin annabi Isa. Kuma bayan mutuwarta, Masar ta faɗa ƙarkashin mamayar Romawa.