Masar ta dakatar da wani farfesa daga aiki kan sukar Annabi Muhammad

Asalin hoton, Getty Images
An dakatar da wani Farfesan ilimin zamantakewa a Masar, bayan zargin da ake yi masa na yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW) yayin da yake gardama da ɗalibansa kan batun aure a Musulunci, da kuma bayyana ra'ayinsa a kafar sada zumunta kan zanen ɓatanci da Mujallar Charlie Hebdo ta yi ga Annabin.
Ɗaliban koyon ilimin zamantakewar sun bayyana ɓacin ransu kan irin kalaman da Farfesa Muhammad Mahdali ya yi yayin da yake bayyana ra'ayinsa.
Tun da farko dai, ɗaliban sun zargi farfesan da yin kalamai marasa daɗi kuma na cin mutuncin Musulunci yayin da yake koyarwa a aji.
A wani bidiyo da aka yaɗa a kafofin sada zumunta, an ga Farfesa Mahdaly na caccakar ayoyin Al-Ƙur'ani a yayin da yake wata tattaunawa kan batun aure da biyan sadaki da kuma saki a Musulunci.
Babu karin bayanai
Ci gaba da duba FacebookBBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba.Karshen labarin da aka sa a Facebook
Daga baya kuma sai ya yi sa-in-sa da ɗalibai a lokacin da yake koyar da su a ji a yayin da suka nemi su taka masa burki kan irin kalaman da yake yi, inda suka ja masa kunne kan cewa ya daina haɗa kalamansa da Al-Ƙur'ani.
A wani bidiyo na daban kuma, an ga farfesan na caccakar yanayin zamantakewar Musulmai inda ya ce abin da suke yi "ba shi da asali". Har ma ya kawo misali da auren mata tara da Annabi Muhammad (SAW) ya yi kuma ya yi kakkausar suka ga Annabin kan hakan.
Wannan katoɓarar da farfesan ya yi kan batun caccakar ayoyin Al-Ƙur'ani da kuma nuna goyon baya ga kalaman Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya harzuƙa mutane da dama musamman a kafofin sada zumunta, inda suke ta caccakar farfesan.
Wasu daga cikin masu amfani da shafin Twitter sun alaƙanta farfesan da mutum mai laLurar "taɓin hankali".
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Wasu kuma na da ra'ayin cewa kwata-kwata ba SHi da addini, kuma bai yaRda da Allah ba.
Daga baya dai Farfesan ya bayar da haƙuri kan abin da ya yi kuma ya goge rubutun da ya yi.
Sai dai ministan ilimin gaba da sakandare a ƙasar ya bayar da umarnin dakatar da Mahdali kuma ya bayar da umarnin ƙaddamar da bincike a kansa.











