Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa za ta ba kwararru damar zama ƴan kasar

Lokacin karatu: Minti 2

A karon farko, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta sanar da cewa za ta fara ba baƙi kuma ƴan ƙasar waje damar zama yan ƙasar, amma sai idan su na da wata ƙwarewar da za ta inganta darajar daular.

Mataimakin Shugaban Daular kuma sarkin Dubai Sheikh Mohammed bin Rashid al Maktoum ne ya bayyana haka, kuma ya ce cikin waɗanda za a ba damar, akwai masu zuba jari da kwararru a wasu fannoni da likitoci da injiniyoyi da kuma ma su wasannin shakatawa kamar mawaƙa.

Ya ƙara da cewa su da iyalansu na iya zama ƴan kasar da ma wata ƙasar ta daban.

Da wuya idan mutane marasa galihu za su sami wannan damar.

Sheikh Mohammed ya ce wannan dama ce ta janyo waɗanda "za su bunƙasa ci gaban kasarmu."

Babu wata tsararriyar hanyar neman zama ɗan ƙasar, sai dai manyan ƴan gidan sarautar ƙasar da manyan jami'an gwamnati ne kawai za su iya bayar da sunan wanda su ke son a ba shi wannan matsayin.

Daga nan ne majalisar ministocin daular za ta yanke hukunci kan amincewa ko kin amincewa da bukatar.

Wannan matakin na zuwa ne yayin da annobar korona ke kara addabar duniya, wanda ya janyo faduwar farashin man fetur , kuma ya tilastawa dubban ƴan ƙasashen waje barin kasar

A 2019, Sheikh Mohammed ya kaddamar da wani shiri na ba mazauna daular wani koren katin da ke ba mai rike da shi damar zama a kasar na tsawon shekara 10.

Amma ba a san ko wannan rukunin mutanen da ke da koren katin na iya amfana da wannan sabon tsarin ba.

Daular na kashe wa yan kasarta biliyoyin daloli wajen samar da ilimi kyauta da kiwon lafiya da bashin mallakar gidaje da tallafin kudi ga 'yan daular da yawansu bai wuce miliyan 1.4 ba.