Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Najeriya: Abin da PDP ta ce kan rahoton cin hanci a gwamnatin Buhari na Transparency International
Babbar Jam'iyyar adawa a Najeriya, PDP, ta mayar da martani game da rahoton da ƙungiyar Amnesty International ta fitar kan cin hanci da ya bayyana Najeriya a matsayin ta 149 a duniya.
Sakataren ƙasa na PDP, Sanata Ibrahim Tsauri ya shaida wa BBC cewa rahoton na ƙungiyar ya tabbatar da almubazzarancin da gwamnatin APC take yi da kuɗaɗen ƴan ƙasar kimanin naira triliyan 15 cikin shekara shida da ta yi kan mulki.
"Akwai takardar da ta fita wadda ta ce a APC kawai an yi almubazzaranci da tiriliyan 9.6, wannan ai ba a ɓoye yake ba, sannan a tuna abin da aka yi a hukumar tara kuɗaɗen haraji ta Najeriya da NEMA da EFCC da kuɗaɗen da aka ce an karɓo," in ji Sanata Tsauri.
Ya kuma ga baiken hukumar EFCC da ke iƙirarin karɓo kuɗaɗn da ake zargin an yi sama da faɗi da su har ma aka kai wasu ƙasashen.
"Suna ina kuɗaɗen, a bincika ita kanta da ta amshi kuɗin mutane in ta ansa, idan da gaske ne ta ansa, ina kuɗin suke, maganar nan ba magana ba ce ta farfaganda, magana ce ta zahiri - an gaza." in ji Sanatan.
Ya ce gwamnatin APC ta yi fice wajen tozarta waɗanda ba ƴan jam'iyyarta ba - wanda ɗan APC ne idan ya yi almubazzaranci shiru ake ba a magana.
A cewarsa, "Duk wanda ka ji an bincika kashi 90 cikin 100, mutanen adawa ne - sai an kama 10 sai a kama ɗaya daga wata jam'iyya sai a sake shi bayan wata ɗaya ko biyu."
Sanatan ya bayyana cewa matsalar cin hanci a Najeriya abu ne da ke farowa daga sama saboda duk kuskuren da aka samu daga sama ne saboda a ganinsa idan na sama ya yi gyara, na ƙasa dole ya bi.
Abin da ya sa cin hanci ke ƙara ta'zzara a Najeriya
A cewar Sanata Tsauri babban dalilin da ya sa cin hanci ke ƙara yin katutu a Najeriya shi ne gazawar gwamnati saboda gwamnati ce da aka gina kan Farfaganda.
"Daman an ci zaɓ ne ba don an shirya ba, ba a iya ba, yau kowa ya gane cewa idan ana son zaman lafiya a Najeriya toh kowa ya koma inda ya fi iyawa." kamar yadda sakataren ƙasa na PDP ɗin ya bayyana.
Yadda za a fitar da Najeriya daga ƙangin cin hanci
Jam'iyyar PDP ta bakin sakatarenta ta kuma ba da shawara kan yadda take ganin Najeriya za ta fita daga matsalar cin hanci. A ganinta, hanyoyi biyu da za a cimma hakan su ne:
Tabbatar da shugabanci na gari
Sanata Ibrahim Tsauri ya ce samar da shugabanci na gari na ɗaya daga cikin abubuwan da ke fitar da ƙasa daga cikin fitina ba a Najeriya kaɗai ba har ma a duniya baki ɗaya.
Ya ce babbar matsalar Najeriya ita ce rashin shugabanci na gari saboda haka "idan ana son a fitar da Najeriya daga wannan hali, sai ƴan Najeriya sun yi wa kansu ƙiyamul laili sun mai da waɗanda suka iya mulki a wurin mulki su mayar da waɗanda suka iya adawa a inda suke adawa."
Duba cancanta wajen ba da aikin yi
A cewarsa, ya kamata a riƙa duba cancanta idan za a ɗauki mutum aiki a Najeriya. "A ba mutum aiki wanda yake iya yi ba a ba shi aiki don shi ƙanin wane ba ne ko ɗan wane bane jikan wane ko kuma ɗan uwan wane." in ji sa.