Sani Abacha: Yadda aka gano biliyoyin kuɗin da tsohon shugaban Najeriya ya sace

A lokacin da tsohon Shugaban mulkin sojin Najeriya ya sace biliyoyin daloli kuma ya mutu kafin kashe kuɗaɗen da ya wawure, lamarin ya sa neman kuɗaɗen cikin shekaru.

Mutumin da aka ɗauka domin mayar da ƙudaɗen ya shaida wa BBC yadda ƙoƙarin gano kuɗaɗen ya mamaye rayuwarsa.

Cikin Satumbar 1999, Lauya Enrico Monfrini ɗan Switzerland ya amsa kiran waya da ka iya sauya shekaru 20 na rayuwarsa.

"Ya kira ni da tsakar dare, ya tambaye ni idan zan iya zuwa ɗakinsa na otal cewa akwai wani abu mai muhimmanci. Sai na ce 'dare ya yi amma gani nan," in ji shi.

Da alama muryar da take magana ta wani babban jami'in gwamnatin Najeriya ce.

'Za ka iya gano kuɗin?'

Mr Monfrini ya ce a lokacin shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya tura jami'in zuwa Geneva domin ya je ya kwaso kuɗaɗen da Abacha ya yi sama-da-faɗi da su mutumin da ya shugabanci ƙasar daga 1993 har zuwa lokacin rasuwarsa a 1998.

A matsayinsa na lauya, Mr Mofrini ya kafa ofishi tun shekarun 1980. "Ya tambaye ni: 'Za ka iya gano kuɗin kuma za ka iya toshe shi? Za ka iya shirya kuɗin yadda za a mayar da su Najeriya?

"Na ce: 'Eh.' Amma a lokacin ban san yadda aikin yake ba. Kuma dole ne na yi saurin koyo, kuma hakan na yi."

Da fari, ƴan sandan Najeriya sun miƙa masa bayanan wasu daga cikin asusun da gwamnatin Switzerland ta rufe waɗanda suke maƙare da kuɗaden da Abacha da makusantansa suka sace, kamar yadda Mr Mofrini ya rubuta a littafin Gano kadarorin da aka sace wato Recovering Stolen Assets.

Ya ce binciken farko da aka yi kuma ƴan sanda suka wallafa a watan Nuwambar 1998, ya gano Abacha da makusantansa sun sace sama da dalar Amurka biliyan 1.5.

Hanyoyin da aka bi wajen wawure kuɗaɗen

Ɗaya daga cikin hanyoyin da aka bi wajen tara maƙudan kuɗin na da firgitarwa.

Abacha zai faɗa wa mashawarcinsa da ya gabatar da buƙatar kuɗi a wajensa domin warware wani batu na tsaro.

Sannan ya sa hannu kan buƙatar da mashawarcin zai miƙa ga babban banki wanda shi kuma zai ba da takardun kuɗin.

Sai mashawarcin ya kwashi kashi mai tsoka na kuɗin ya kai gidan Abacha.

Wannan ɗaya ce daga cikin hanyoyin da Abacha da mashawarcinsa suka wawushe maƙudan kuɗaɗe. Sauran hanyoyin sun haɗa da yin aringizon kwangiloli da ake bai wa abokai sannan a dafe rarar da aka samu a kuma nemi kwamfanonin ƙetare su ba da cin hanci domin ba su damar gudanar da harkokinsu a ƙasar.

An shafe shekara uku ana wannan badaƙala har sai da komai ya sauya lokacin da Abacha ya mutu yana da shekara 54 a ranar 8 ga watan Yunin 1998.

Babu tabbacin ko ya samu bugun zuciya ne ko kuma guba aka sa masa saboda ba a yi bincike kan gawarsa ba, kamar yadda likitan Abacha ya fada wa BBC.

Abacha ya mutu ne kafin ya kashe kuɗaɗen sannan bayanan wasu bankuna ƙalilan sun ba da haske kan inda aka ɓoye kuɗaɗen.

"Takardun da ke ɗauke da bayanan asusun sun ba ni haske na gano wasu asusun," in ji Mr Monfrini.

Samun waɗan nan bayanai ya sa ya gabatar da batun ga Atoni Janar na Switzerland.

Kuma sai aka yi nasara. Mr Monfrini ya bayyana cewa iyalan Abcha da makusantansa sun kafa ƙungiyar masu laifi.

Wannan babban lamari ne saboda ya sake ba da kafar duba wasu hanyoyin da hukumomi za su iya tafiyar da asusun bankinsu.

Wane ne Abacha?

  • Ya yi yaƙin basasa ƙarƙashin rundunar sojin Najeriya
  • Ya taka rawa a juyin mulkin da aka yi har guda biyu kafin ya zama ministan tsaro a Agustan 1993
  • Ya zama shugaban ƙasa sakamakon juyin mulkin da aka yi a Nuwambar 1993
  • An zargi gwamnatinsa da take haƙƙokin bil adama
  • An dakatar da Nigeria daga Ƙungiyar Ƙasashe renon Ingila bayan yanke wa masu fafutukar tabbatar da haƙƙin bil adama hukuncin kisa su tara a 1995
  • Ya rasu ranar 8 ga watan Yunin 1998 yana mai shekara 54
  • Yana da ƴaƴa 10

Atoni Janar ɗin ya ba da sanarwa ga duka bankunan Switzerland inda ya buƙaci su ba da bayanin ko akwai asusun da aka buɗe da sunan Abacha da makusantansa.

"Cikin sa'a 48, kashi 95 na bankunan da sauran cibiyoyin kuɗi suka bayyana abin da suke da shi wanda da alama mallakin iyalin Abacha ne."

Wannan kuma zai bankaɗo wasu asusun bankin da ake ajiyarsu a faɗin duniya.

"Bankuna suka gabatar da takardu ga mai gabatar da ƙara a Geneva kuma ni ina yin aikin mai gabatar da ƙara saboda ba shi da lokacin yin aikin," Mr Mofrini ya shaida wa BBC.

'Asusan banki sun yi ta aman kudi'

"Muna gano inda kuɗin ya fito da kuma inda yake zuwa.

"Bayyana shige da ficen kuɗaɗen a waɗan nan asusun bakin ya ƙara ba ni ƙarin bayani game da wasu ƙuɗaɗen da aka karɓa daga wasu ƙasashen aka kuma tura wasu ƙasashe.

"Lamarin ya fara ne da asusu ƙalilan sannan aka riƙa buɗe wasu asusun bankin.

"Muna da hujjoji sosai kan kuɗaɗen da ake turawa wurare daban-daban, Bahamas da Nassau da Tsibirin Cayman."

"Babu wanda ya gane yadda abin yake aiki. Sai da na biya mutane da dama kuɗi, da akntoci da dama da lauyoyi a ƙasashe daban-daban."

Mr Monfrini ya amince zai karɓi kashi huɗu na kuɗaɗen da aka mayar Najeriya - abin da ya ce ba su taka kara sun karya ba."

Gano kuɗaɗen sai ya zama cikin sauri idan aka kwatanta da yadda aka samu mayar da su zuwa Najeriya.

"Iyalin Abacha sun yi ta roƙo kan abin da muka yi. Wannan ya janyo tsaiko na tsawon lokaci.

Jinkirin da aka sake samu kuma ya faru ne yayin da ƴan siyasar Switzerland suke jayayya kan ko ma za a sake sama da faɗi da kuɗaɗen ne idan aka mayar da su.

An mayar da wasu daga cikin kuɗaɗen bayan shekara biyar.

Mr Monfrini ya rubuta a 2008 cewa an aike $508m da aka gano a asusun banki da dama da sunan Abacha a Switzerland zuwa Najeriya tsakanin 2005 da 2007.

Zuwa 2018, adadin kuɗaɗen da aka mayar wa Najeriya daga Switzerland ya zarce $1bn.

Sauran ƙasashe na jan ƙafar mayar da kuɗaɗen.

"Liechtenstein, misali, wani mafarki ne."

A Yunin 2014, Liechtenstein ya mayar wa Najeriya $277m.

Bayan shekara shida kuma, cikin Mayun 2020, aka sake mayar wa Najeriya $308m da ke cikin wani asusu a Jersey. Hakan ya zo ne bayan da hukumomin Najeriya suka amince za a yi amfani da kuɗaɗen musamman wajen gina gadar Second Niger da babbar hanyar Legas zuwa Ibadan da kuma hanyar Abuja zuwa Kano.

Har yanzu Mr Monfrini na sa ran za a maida $30m da ke ɓoye a Burtaniya tare da ƙarin $144m da ke ajiye a Faransa da kuma wata ƙarin $18m a Jersey.

A cewarsa, a jumulla, aikin da ya yi ya taimaka wajen gano sama da $2.4bn.

"Da farko mutane na cewa Abacha ya sace kimanin $4 zuwa $5bn. Ba na tunanin haka abin yake. Ina ganin mun yadda da akasarin abin da suka faɗa."