Kullen Capitol a Amurka: Jami'an tsaron Capitol sun yi shirin ko ta kwana gabanin rantsar da Biden

Asalin hoton, Reuters
Kwana biyu gabanin rantsar da Joe Biden a matsayin shugaban Amurka, an kulle harabar ginin majalisar dokokin kasar a birnin Washington DC na ɗan taƙaitaccen lokaci, bayan bayanan sirri.
Ƴan sanda sun ce sun ɗauki matakin ne a matsayin na riga-kafi, bayan wasu shaidu sun ce sun ga hayaƙi yana tashi a kusa da wajen.
An kuma ɗage shirin gwajin rantsar da Biden ɗin.
Mutum biyar ne suka mutu bayan magoya bayan Trump sun mamaye ginin na Capitol, wanda a nan zauren Majalisun Amurka yake.
An tura dubban sojojin ko-ta-kwana na National Guard harabar ginin, da kuma tsakiyar birnin Washington DC.
Hukumomi sun ce babu wata barazana ga jama'a. A yanzu haka ƴan majalisar suna hutu kuma ba za su koma ba har sai bayan bikin rantsuwa a ranar Laraba.
Wadane irin shiye-shirye ake yi na rantsar da Biden?
An tsaurara tsaro bayan masu zanga-zangar sun afka wa ginin a farkon watan nan.
An rufe lambun wajen wanda ake kira The National Mall tare da manyan hanyoyi da dama. An kuma sanya shinge a kewayen fadar White House.
Tuni aka ɗage gwajin rantsuwar da aka shirya yi ranar Litinin saboda dalilan tsaro.
Saboda cutar korona za a taƙaita yawan mutanen da za su halarci bikin rantsuwar ranar 20 ga watan Janairu. Tikiti 1,000 kawai aka raba, maimakon 200,000 da aka saba rabawa.
Duka jihohin Amurka 50 da kuma birnin Washigton DC suna cikin shirin ko-ta-kwana saboda yiwuwar mummunar zanga-zanga.
Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka ta yi gargaɗin yiwuwar samun zanga-zangar mutane masu ɗauke da makamai a duka majalisun jihohi.
Da zarar an rantsar da shi, Mista Biden zai ba da umarnin soke matakin Trump na hana ƴan wasu ƙasashe shiga Amurka da koma yarjejeniyar Paris ta sauyin yanayi.
Ana sa ran shugaban mai jiran gado zai mayar da hankali kan haɗa iyalan da iyakar Amurka da Mexico ta raba, sannan zai sanar da dokar sanya takunkumi saboda cutar korona.
Me zai faru ranar ranar 20 ga Janairu?
Mista Biden shugaba mai jiran gado da Kamala Harrris, za su yi rantsuwar kama aiki a gaban ginin majalisar dokoki, Capitol, suna fuskantar lambun National Mall daga samansa.

Asalin hoton, Reuters
Da zaran an rantsar da su, Mista Biden zai yi jawabin kama aiki, inda zai bayyana abin da zai mayar da hankali a shugabancinsa.
Bikin ya haɗa da rera waƙoƙi, da ɗaukar alƙawarin biyayya da kuma add'a. Lady Gaga ce za ta rere taken ƙasa, sannan Jennifer Lopez za ta rera waƙa.
Wani hamshaƙin mutum zai ragewa taron armashi da rashin zuwansa: Mista Trump ya ce ba zai halarci bikin rantsuwar ba.
Tom Hanks zai jagoranci wani shiri na talabijin a daren na 20 ga Janairu, inda Justin Timberlake da Bon Jovi za su gabatar da waƙoƙi.











