Musulmin da suka samar da rigakafin korona

Asalin hoton, BIONTECH
Matar da mijin, waɗanda 'yan asalin Turkiyya ne, sun zamo na farko da suka fara samar da riga-kafin cutar korona wanda babban abin alfahari ne.
Ugur Sahin mai shekara, 55 shi ne shugaban kamfanin bincike da samar da magunguna na ƙasar Jamus mai suna BioNTech.
Ya kafa kamfanin ne tare da matarsa Özlem Türeci mai shekara 53 tare da wani tsohon malaminsa Farfesa Christoph Huber, ƙwararre a ɓangaren cutar Daji kuma ɗan Austria.
Farfesa Sahin da Dakta Türeci sun kafa kamfanin BioNTEch ne a shekarar 2008 a birnin Mainz a yammacin Jamus.

An haifi Dakta Ugur Sahin ne a garin Iskenderun na Turkiyya.
Yana da shekara huɗu iyayensa suka koma birnin Cologne na Jamus inda iyayensa suka yi aiki a kamfanin ƙera motoci na Ford.
Ya girma da burin zama likita, kuma ya cika burinsa a jami'ar Cologne. A 1993 ne ya gama digirinsa na uku a jami'ar kuma ya karanci fannin yadda ƙwayayen halitta ke rikiɗa su zama daji.
Ya bayyana cewa a lokacin da yake jami'a ya kan tsaya a ɗakin gwaji har sai dare ya tsala kafin ya tafi gida a kan kekensa.
Tun farkon fara aikin likita ya haɗu da Dakta Özlem wadda ita ma take da burin zama likita.
An haifi Dokta Özlem ne shekara 53 da suka gabata a Jamus, kuma mahaifinta likita ne amma ɗan asalin Turkiyya da ya koma Jamus daga Istanbul.
"Ban taɓa tunanin zan iya wani aiki da ba na likita ba tun ina ƴar ƙarama," a cewarta.
Sun yi aure a shekarar 2002 lokacin Farfesa Sahin yana aiki da asibitin koyarwa na Jami'ar Mainz.
Ko a ranar bikinsu, sai da Farfesa Sahin da Dakta Özlem suka je ɗakin gwaji don gudanar da bincike bayan da taron ƴan biki ya watse.
A yanzu, kamfaninsu na BioNTech na da ma'aikata 1,300 daga ƙasashe sama da 60, kuma fiye da rabin ma'aikatan mata ne a cewar jaridar Deutsche Welle ta Jamus.
A watan farko da cutar korona ta bayyana, Farfesa Sahin ya karanta yadda cutar take yaɗuwa a China a mujallar The Lancet sai ya fahimci irin illar da ta ke yi kuma ya yi hasashen za ta iya zama annobar duniya.
Nan da nan ya ɗauki ma'aikata sama da 400 don fara aiki kan riga kafin cutar.
"Ni ban damu da kuɗin da zan samu ba," ya shaida wa jaridar Wirtschaftswoche.
"Muna so mu kafa cibiyar bincike mu samar da magunguna. Muna so mu shafi rayuwar mutane. Ni abin da ya dame ni kenan," a cewarsa.
Kafin barkewar annobar korona, BioNTech na gudanar da bincike ne kan magungunan cutar daji, amma kawo yanzu kamfanin bai yi nasarar kai wa matakin da za a amince da waɗannan magungunan ba.

Asalin hoton, AFP
BioNTech da kamfanin samar da magunguna na Amurka Pfizer sun sanar da riga-kafinsu wanda ke iya kare mutum daga kamuwa da cutar korona da kusan kashi 90 cikin 100.
Ba a taɓa samar da riga-kafi cikin gaggawa irin haka ba baya. Sau da yawa, bincike da gwaje-gwajen riga-kafin na dogara ne da idan sun yi aiki tsawon shekaru 7 ko 8.
Amma an yi wa tawagar da ta samar da riga-kafin covid-19 a kamfanin BIoNTech inkiya da 'Masu Tsananin Sauri' saboda yadda suke aiki cikin gaggawa.
A yanzu, darajar kamfanin BioNTech ya kai dala biliyan 21 a kasuwar hannun jarin Nasdaq ta New York a Amurka, wanda a bara darajarsa bai wuce dala biliyan 4.6 ba.
Farfesa Sahin wanda shi ne shugaban kamfanin na da kashi 18 cikin 100 na kamfanin kuma a halin yanzu yana cikin mutane 10 mafiya arziƙi a Jamus. Matarsa Dakta Özlem ita ce babbar likita a cibiyar.










