Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
EFCC ta fusata 'yan Twitter kan holen mutanen da ake zargi da damfara
Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati, ta gamu da fushin masu amfani da shafin Twitter bisa yin holen wasu mutane da ake zargi da yin damfara.
A ranar Litinin ne EFCC ta wallafa hotuna a shafinta na Twitter na wasu matasa goma da ta ce ta kama a birnin Lagos bisa zarginsu da yin damfara a shafukan intanet.
Mutanen da take zargin su ne Jonathan Daniel Adebayo, Lawal Waidi Seun, Adeosun Joseph, Taiwo Gbemileke, Oseni Omotayo, Emmanuel Fakiyesi, Rasheed Ogunlana, Oladunni Segun, Sowunmi Rotimi da kuma Efetobore Prince Wilfred.
Hukumar ta EFCC ta ce an kama mutanen ne ranar Asabar, 9 ga watan Janairu 2021 lokacin da aka kai musu samame da sanyin safiya a yankin Alagbado da ke birnin Lagos, sakamakon bayanan sirrin da aka tsegunta wa hukumar kan laifukan da ake zarginsu da aikatawa.
Martanin 'yan Twitter
Sai dai wannan batu ya ja hankalin masu amfani da Twitter wadanda suke gani bai dace a rika yin holen mutanen da ake zargi da aikata laifuka ba tun da ba a gurfanar da su gaban kotu ta kama su da laifi ba.
Da yake tsokaci kan batun, fitaccen dan jaridar nan na Najeriya, Cif Dele Momodu, ya bai wa EFCC da sauran jami'an tsaro shawara da su daina gaggawar "yin holen hotunan matasa 'yan Najeriya a shafukan sada zumunta" idan ba su gurfanar da su a gaban kotu ta tabbatar da abin da ake zarginsu da aikatawa ba.
Ya kara da cewa yin hakan zai iya yin illa ga martabar mutanen da aka yi holensu ko da kuwa daga baya an gano ba su da laifi.
Shi kuwa wanda yake kiran kansa Black Eagle ya ce EFCC tana nuna rashin iya aiki domin babu abin da take yi "sai ta kama mutane barkatai, ta yi musu barazanar samunsu da laifin cin hanci.. ba tare da cikakken bincike ba".
A nasa bangaren, Timothy Integrity ya ce EFCC ba ta gurfanar da mutanen da ta kama a gaban kotu ba amma tuni ta yi holensu, me ya sa ba ta yi holen tsohon shugabanta Ibrahim Magu ba wanda shi ma aka zarga da aikata ba daidai ba.
Abin da doka ta ce
Masana harkokin shari'a sun sha bayyana cewa hukumomin tsaro ba su da hurumin yin holen mutanen da suke zargi da aikata laifi.
Wani fitaccen lauya da ke Kaduna a arewacin Najeriya, Barista El-Zubair Abubakar ya shaida wa BBC cewa yin holen mutanen da ake zargi daidai yake da take hakkokinsu.
A cewarsa, "sashe na hudu na kudin tsarin mulkin Najeriya ya zayyana hakkokin bil adama da suka hada da kada a ci mutuncin dan adam, kuma galibi idan an yi holen mutum bisa wani laifi daga baya wasu ana wanke su amma duniya ba ta sani ba don haka wannan tabon da aka yi musu ba zai goge ba."
Shi ma Barista Muhammad Al-Gazali, wani lauya shi ma da ke Kaduna, ya ce yin holen mutanen da ake zargi da aikata laifi ya saba wa sashe na 36 kundin tsarin mulki da ya nemi a saurari dukkan bangarori kafin daukar wani mataki.
Ya kara da cewa ya kamata hukumomi irin su EFCC su rika gudanar da cikakken bincike sannan su gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu wadda ita ke da damar yanke hukunci bisa yin la'akari da kwararan shaidu da hujjoji.