Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jirgin fasinja ya ɓace jim kaɗan bayan tashinsa a Indonesia
Wani jirgin fasinja ɗauke da mutum 50 ya ɓace jim kaɗan bayan tashinsa daga babban birnin Indonesia, Jakarta.
Jirgin na Boeing 737 mallakar kamfanin Sriwijaya Air, an daina jin ɗuriyarsa ne lokacin da yake kan hanyar zuwa Pontianak da ke yankin West Kalimantan, a cewar hukumomi.
Shafin da ke bin diddigin jiragen sama Flightradar24.com ya ce jirgin ya yi tafiyar mita 3,000 (ƙafa 10,000) cikin ƙasa da minti ɗaya yayin da yake gangarowa ƙasa.
Waɗanda suka gane wa idonsu hatsarin sun ce sun ji ƙarar fashewa.
Wani masunci mai suna Solihin ya faɗa BBC Indonesian cewa ya ga hatsarin kuma matuƙin jirgin ya yanke shawarar ya saukar da jirgin ne.
"Jirgin ya faɗo kamar aradu a cikin teku kuma ya tarwatse a cikin ruwa," in jni shi.
"A kusa da mu ne sosai, ɓaraguzan jirgin sun kusa sauka kan jirgin ruwana."
Ma'aikatar sufuri ta ce an fara ayyukan ceto.
Kamfanin zirga-zirgar cikin gida na Sriwijaya Air ya bayyana cewa yana ci gaba da tattara bayanai game da jirgin.
Jirgin ba ƙirar 737 Max ba ne, jirgin kamfanin Boeing wanda ya sha yin hatsari a cikin 'yan kwanakin nan.
Hatsarin farko ya faru ne a watan Oktoban 2018, inda jirgin Indonesian Lion Air ya faɗa cikin ruwa tare da kashe mutum 189 da ke cikinsa.