Donald Trump: An rufe shafin Twitter na shugaban Amurka

Kamfanin Twitter ya ce ya dauki matakin ne bayan nazari kan abubuwan da shugaban na Amurka ya wallafa a shafin nasa, da kuma abin da suke nufi.

Gabanin haka dai an dakatar da shafin nasa ne na tsawon sa'a 12.

Daga nan ne kuma kamfanin ya yi gargadin cewa zai rufe shafin na shugaba Trump baki daya matukar ya karya ka'idojin kamfanin.

Lokacin da ya mayar da martani kan rufe shafin, mai bai wa shugaba Trump shawara kan yakin neman zabe Jason Miller ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa wannan "Abin takaici ne... idan kana tunanin cewa ba za su kawo kanka ba to ka yi kuskure."

Rufe shafin tuwita na Donald Trump din ya zo ne bayan kalaman da ya wallafa a shafin nasa ranar Larabar da ta gabata, inda ya bayyana wadanda suka kutsa cikin ginin majalisar dokokin kasar a matsayin ''yan kishin kasa'.

Daruruwan magoya bayansa ne suka suka kutsa kai cikin ginin majalisar dokokin kasar da ke Washington a daidai lokacin da 'yan majalisar ke yunkurin tabbatar da nasarar zababben shugaban kasar Joe Biden.

Hargitsin ya haifar da mutuwar farar hula 4 da jami'in dansanda 1.

Wannan mamaye da aka yi wa majalisar ya zo ne jim kadan bayan Trump ya yi jawabi ga magoya bayansa, inda ya ce "Ba za mu saduda ba, ba za mu amince da shan kaye ba."